Ilimi
KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta
Daga Khadijah Aliyu
Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar da yaran da ba sa zuwa makaranta cikin tsarin karatu da kuma mayar da waɗanda suka daina zuwa makaranta.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Ungogo, Alhaji Tijjani Amiru ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da shirin wayar da kan jama’a kan shigar da yara makaranta da kuma mayar da waɗanda suka daina zuwa makaranta, a garin Zaura da ke Ungogo.
Ya bayyana ilimi a matsayin ginshiƙin ci gaban al’umma, tare da kira ga iyaye da su tabbatar sun shigar da ‘ya’yansu makaranta, sannan su mayar da waɗanda suka daina zuwa domin ci gaba da karatunsu.
Alhaji Tijjani ya yaba wa masarautu da shugabannin addinai bisa goyon baya da gudummawar da suke bayarwa wajen yaƙin neman shigar da yara makaranta a yankin.
Sakatariyar Ilimi ta Ƙaramar Hukumar Ungogo, Hajiya Hussaina Ibrahim, ta yi kira ga iyaye da malamai da su riƙa sa ido kan zuwan ɗalibai makaranta domin hana yawon barin makaranta.
Ta yaba wa shugaban ƙaramar hukumar bisa jajircewarsa wajen bunƙasa ilimi, tare da kira ga daidaikun mutane da ƙungiyoyi da su taimaka wajen tallafa wa ƙoƙarin gwamnati na inganta ɓangaren ilimi.
Dagacin Zaura ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa farfaɗo da harkokin ilimi ta hanyar shirin ilimi kyauta na jihar.
Ya kuma yaba wa Ƙaramar Hukumar Ungogo bisa kai shirin wayar da kan jama’a game da shigar da yara makaranta zuwa Zaura, tare da alƙawarin ci gaba da bayar da goyon baya domin ganin shirin ya yi nasara.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, a wani yunƙuri na farfaɗo da harkokin ilimi, Gwamnatin Jihar Kano ta bullo da tsare-tsare da shirye-shirye daban-daban domin tabbatar da samar da ilimi kyauta kuma wajibi a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
