Connect with us

Labarai

Gwamna Dauda Lawal Ya Ƙaddamar Da Gina Hanyar Kilomita 95 A Tsafe Don Ƙarfafa Ayyukan Tsaro

Published

on

Daga Aminu Dalhatu, Gusau

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya ƙaddamar da aikin gina sabuwar hanya mai tsawon kilomita 95 a Ƙaramar Hukumar Tsafe, yana mai cewa aikin zai inganta zirga-zirgar kayayyaki da ayyuka tare da ƙarfafa ayyukan jami’an tsaro a yankin.

 

Gwamna Lawal ya ƙaddamar da aikin ne a ranar Lahadi, inda aka fara gina hanyoyin ’Yandoton Daji da Cediya da Doka da ’Yan Waren Daji da Hayin Alhaji Bedi da Unguwar Joji da ’Yankuzo zuwa Tsafe, tare da gina gadoji guda biyar a Ƙaramar Hukumar Tsafe.

 

An raba aikin zuwa matakai biyu, inda kamfanin SKY Construction Company ya samu kwangilar matakin farko mai tsawon kilomita 47, yayin da Setraco Construction Company Limited zai gudanar da mataki na biyu mai tsawon kilomita 48.

 

Da yake jawabi yayin ƙaddamar da aikin, Gwamna Lawal ya ce hanyar ta ratsa wasu al’ummomi da galibinsu manoma ne, waɗanda ke taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasar tattalin arzikin Jihar Zamfara.

 

Ya ce gwamnatin jihar ta ɗauki alhakin kare rayuka da dukiyoyin jama’a da muhimmanci, shi ya sa ta sanya aikin hanyar cikin manyan ayyukan da za su taimaka wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Zamfara.

 

“Gwamnatin da ke da alhaki ta himmatu wajen tabbatar da tsaro da walwalar al’ummarta. Shi ya sa muka ba wannan aikin hanya muhimmiyar fifiko a matsayin wani babban mataki na dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Zamfara,” in ji shi.

 

Gwamnan ya ce sake gina hanyar zai sauƙaƙa zirga-zirgar kayayyaki tare da inganta tafiye-tafiyen jami’an tsaro, abin da zai ƙara musu ƙarfin gudanar da ayyukansu da kuma saurin kai ɗauki yayin fuskantar barazana ko hare-hare.

 

Ya bayyana aikin a matsayin wani ɓangare na babban shirin farfaɗo da ababen more rayuwa a faɗin jihar.

 

A cewarsa, daga hanyar Gusau–Magami–Dansadau zuwa hanyar Zurmi–Rukudawa, da kuma hanyar Mallamawa–Bukkuyum wadda ke da reshe zuwa Masamar Mudi, gwamnatin jihar na ci gaba da haɗa al’ummomi da juna tare da magance gibin ababen more rayuwa da aka daɗe ana fama da shi.

 

Gwamna Lawal ya ce gwamnati ta fahimci muhimmancin ingantattun hanyoyi wajen tabbatar da zirga-zirga cikin aminci, sauƙaƙa safarar kayayyaki da bunƙasa tattalin arziki.

 

Ya ƙara da cewa manufar aikin ba ta tsaya ga samar da hanyar sufuri kaɗai ba, domin ana sa ran zai ƙara haɓaka harkokin tattalin arziki, inganta tsaro da kuma kyautata rayuwar al’ummomin da aikin ya shafa.

 

“Mun fahimci irin gaggawar da ake da ita saboda mawuyacin halin da waɗannan al’ummomi ke ciki, kuma mun ƙuduri aniyar bin jadawalin aikin yadda ya kamata domin tabbatar da kammala shi cikin lokaci,” in ji Gwamnan.

 

Gwamna Lawal ya kuma umarci Ma’aikatar Ayyuka da Bunƙasa Ababen More Rayuwa da ta tabbatar da tsauraran matakan sa ido kan aikin, tabbatar da inganci da kuma bin ƙa’idojin aikin injiniya da aka amince da su a duk tsawon lokacin gudanar da aikin.

 

Ya ce kamfanonin da suka samu kwangilar ayyukan gwamnati dole ne su fahimci cewa Gwamnatin Jihar Zamfara na buƙatar a samu cikakken amfani da kuɗin da aka kashe, ingantaccen aiki da kuma ababen more rayuwa da za su iya ɗorewa na dogon lokaci.

 

“Ina fatan wannan hanya za ta inganta sufuri da tsaro, ta zama wata gada da za ta ƙara haɗa al’ummomi wuri guda, tare da zama alamar ƙudirinmu na bunƙasa ababen more rayuwa domin ci gaba da wadata Jihar Zamfara,” in ji Gwamna Lawal.

Fassara: Shafii Abubakar Wababe

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara