Fasaha
Jigawa Ta Amince Da Faɗaɗa Kamfanin Hada Batura Na Lithium
Daga Usman Muhammad
Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da faɗaɗa shirin kafa kamfanin hada na’urar hasken rana ta solar, ta yadda zai ƙunshi kamfanin hada batirin lithium na adana makamashi.
Kwamishinan Yaɗa Labarai, Alhaji Sagir Musa Ahmed, ne ya bayyana hakan jim kaɗan bayan kammala taron majalisar zartarwar jihar da aka gudanar a Gidan Gwamnati da ke Dutse.
Ya ce ƙara hada batirin lithium na adana makamashi zai samar da cikakken tsarin samar da kayayyakin makamashi masu amfani da hasken rana cikin inganci.
A cewarsa, hakan zai sanya Jigawa ta zama cibiyar da ake hada kayayyakin hasken rana da na adana makamashi, waɗanda za su hidimtawa jihar da sauran wurare.
Sagir ya ce faɗaɗa aikin zai ƙara darajar tattalin arzikin shirin ga jihar, tare da ƙara yawan kayayyakin makamashi da za a riƙa haɗawa a cikin gida.
Ya ƙara da cewa aikin zai samar da guraben ayyukan yi ga ƙwararru, da damar horas da ma’aikata kan fasahar zamani, tare da tallafa wa kasuwancin da ke cikin harkar makamashi.
Kwamishinan ya ce shirin ya yi daidai da ƙudirin gwamnatin Gwamna Umar Namadi na faɗaɗa masana’antun jihar da kuma bunƙasa samar da makamashi mai ɗorewa.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
