Labarai
Zamu Horas Da Manoma Kan Amfani Da Sinadaran Noma -NWDC
Hukumar Raya Yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya na nazarin yiwuwar haɗin gwiwa da Wani kamfani, Global Chemical Security and Safety Consultancy domin horar da manoma kan yadda za su yi amfani da sinadaran noma cikin aminci, tare da inganta samar da abinci a yankin.
Manajan Daraktan Hukumar, Farfesa Shehu Abdullahi Ma’aji, ne ya bayyana haka yayin da ya karɓi tawagar shugabannin kamfanin, ƙarƙashin jagorancin wanda ya kafa shi kuma Babban Jami’in Gudanarwarsa, Dakta Mustapha Tijani Usman, a ziyarar ban-girma da suka kai masa.

A cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Hukumar, Abdulrashid Yusuf Safana, ya fitar, tawagar ta gabatar da wani tsari na horar da manoma a aikace kan amfani da sinadaran noma cikin aminci domin samun ingantaccen amfanin gona a jihohin Arewa maso Yamma guda bakwai.
Dakta Usman ya ce kamfanin na Bada matakan Kariya da bada shawarwari tare da ingantaccen tsari ga manoma don ɗorewar amfani da sinadarai ta hanyar bayar da horo na ƙwarewa da gudanar da bincike da nazari da sa ido da tantance yadda ake amfani da sinadaran.
Ya ce haɗin gwiwar da ake shirin yi zata ƙarfafa manoma wajen amfani da sinadaran noma yadda ya kamata, tare da bunƙasa harkar noma, wadda ke da matuƙar muhimmanci wajen samar da wadataccen abinci da tabbatar da zaman lafiya a yankin.
Yayin gabatar da shirin, Daraktan Kula da Sinadarai da amfaninsu Cikin aminci, Mista Buba Shanu, ya ce shirin zai sake horas da manoma kan yadda ya kamata su yi amfani da magungunan kashe ciyawa dana kashe ƙwari da takin zamani da sauran sinadaran noma.
Mista Shanu ya bayyana raguwar ingancin ƙasa da matsin lamba kan filayen noma da kuma rashin amfani da kayan aikin noma yadda ya kamata a matsayin manyan matsalolin da ke barazana ga manoma da muhalli.
Ya ce manoma da dama ba su da isasshen ilimi kan adadin sinadaran da ya kamata su yi amfani da su da yadda ake sarrafawa da adanawa da lokacin da ya kamata a dakatar da amfani da sinadari kafin girbi, da kuma matakan kare lafiyar mutume.
Ya ƙara da cewa ƙwarewar kamfanin a fannin takin zamani, ciki har da aiki a tsohon Kamfanin Takin Zamani na Ƙasa (NAFCON), ce ta ƙarfafa fafutukarta wajen wayar da kan jama’a game da amfani da sinadaran noma cikin aminci.
A cewarsa, horon zai taimaka wajen ƙara yawan amfanin gona da rage haɗarin da ke tattare da lafiya da kare muhalli da kuma dakile amfani da sinadaran noma ba bisa ƙa’ida ba, wanda ka iya haifar da matsalolin tsaro.
Ana sa ran shirin zai yi amfani da tsarin horo na aikace-aikace kai tsaye a gonaki, domin isa ga manoman karkara a sassan jihohin Arewa maso Yamma.
Da yake mayar da jawabi, Farfesa Ma’aji ya ce shirin ya yi daidai da manufofin Hukumar na bunƙasa noma da tabbatar da wadatar abinci da haɓaka da kuma ƙarfafa al’umma.
Ya bayyana cewa rashin tsaro da ƙarancin yawan amfanin gona da kuma zaman kashe wando ko rashin aikin yi tsakanin matasa matsaloli ne da ke da alaƙa da juna, yana mai cewa shirye-shiryen da za su inganta aikin noma cikin aminci da ɗorewa za su iya taimakawa wajen samar da zaman lafiya da ci gaba.
Farfesa Ma’aji ya tabbatar wa tawagar cewa Hukumar za ta duba shirin tare da samar da tsarin da zai ba da damar gudanar da haɗin gwiwa idan hakan ya samu karɓuwa.
Ya ce NWDC za ta ba da fifiko ga haɗin gwiwar da ke samar da sakamako mai amfani da inganta tsaro da kuma samar da ayyukan yi ga matasa da mata a aikin gona.
Gyarawa Yusuf Zubairu. Fassara: Shafii Abubakar Wababe
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
