Labarai
Kungiyoyin Agaji Sun Zargi Isra’ila Da Hana Shigar Da Kayan Jin Kai Zuwa Gaza
Ƙungiyoyin agaji fiye da 100 sun zargi Israila da ci gaba da hana shigo da kayan jin kai cikin Gaza duk kuwa da alƘawarin da ta yi na bada damar shigo da kayan agaji masu yawa domin sauƘaka matsalar yunwa.
ƙungiyar agaji ta Oxfam ta ce an hanata shigo da kayan agaji da aka yi ƙiyasin sun fi dala miliyan biyu, yayin da ƙungiyar agaji ta Care ta ce akwai kayan agaji na iyaye mata da jarirai da suka shafe tsawon wata biyar suna jiran su shigo da su Gaza wanda kuɗinsu ya zarce dala miliyan guda.
Ƙungiyoyi masu yawa sun ce ba a samu ko da mota ɗaya daga cikin manyan motocinsu da Isra’ila ta bari ya shiga cikin Gaza tun watan Maris daya gabata .
Ƙungiyoyin agajin sun yi gargaɗi kan sabbin dokokin tantancewa na israila , na hana su samun damar shiga cikin Gazan
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
