Kasuwanci
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Zamfara Ta Bada Ingataccen Tsaro A Gabanin Zaben Cike Gurbi Na Kaura Namoda Ta Kudu.
A shirye shiryen zaben cike gurbi na dan majalisar dokokin jihar na Kaura Namoda ta kudu dake tafe, kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara, Ibrahim Balarabe Maikaba, ya kai wata muhimmiyar ziyarar tantance tsaro a karamar hukumar Kaura Namoda.
A yayin ziyarar, CP Maikaba ya gudanar da taro da daukacin jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki a yankin domin tattaunawa kan matsalolin tsaro da ake fama da su tare da tsara hanyoyin da za a bi domin ganin an gudanar da zaben cikin sauki.
Kwamishinan ya kara jaddada kudurin rundunar na ganin an dawo da zaman lafiya ba kawai a Kaura Namoda ba har ma a fadin jihar.
Ya kuma bai wa mazauna yankin tabbacin shirin rundunar na samar da isasshen tsaro kafin, lokacin da kuma bayan zaben fidda gwani.
CP Maikaba ya kuma yi kira da a ci gaba da bayar da goyon baya da hadin kan shugabannin al’umma da mazauna yankin wajen yakar duk wani nau’in miyagun laifuka.
Ya jaddada cewa, rundunar ta ci gaba da jajircewa a kokarinta na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ga dukkan ‘yan kasa.
AMINU DALHATU.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
