Labarai
Yan Syria Masu komawa gida na Fargabar bama-bamai da aka binne a Kasa
Ƴan Syria da suke komawa gidajensu bayan yaƙin basasar ƙasar ya yi sauƙi a sanadiyar hamɓarar da gwamnatin Assad, suna cike da fargabar bama-bamai da aka binne a ƙarƙashin ƙasa.
Aƙalla mutum 144, ciki har da ƙananan yara 27 ne suka rasu a sanadiyar ragowar bama-baman da aka yi amfani da su a lokacin yaƙin daga lokacin da aka hamɓarar da gwamnatin Bashar al-Assad a watan Disamba, kamar yadda ƙungiyar Halo Trust ta ruwaito.
Jami’an tsaron White Helmets na Syria sun bayyana wa BBC cewa yawancin waɗanda suka rasu manoma ne da suka fara komawa gonakinsu.
Hassan Talfah, wanda yake jagorantar sashen tsince bama-bamai a arewa maso yammacin ƙasar, ya ce nau’in UXO waɗanda ba a ƙarƙashin ƙasa suke ba, sun fi sauƙin sha’ani, sannan ya ce tsakanin Nuwamban bara zuwa 3 ga Janairu sun ctsince aƙalla bama-bamai 822.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai23 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
