Labarai
RAMADAN: Gwamnatin Jigawa Ta Rage Lokutan Aiki Ga Ma’aikatan Jihar
Gwamna Umar Namadi ya amince da rage lokutan aiki ga ma’aikatan gwamnati a Jihar Jigawa yayin azumin Ramadan na 2025.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da aka fitar kuma aka rabawa manema labarai aDutse, wacce Babban Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ya sanya wa hannu.
“Farawa daga yanzu, ma’aikatan gwamnati a jihar za su rika fara aiki da karfe 9:00 na safe kuma su tashi da karfe 3:00 na yamma daga Litinin zuwa Alhamis, raguwar awanni biyu daga tsohon lokacin rufewa na karfe 5:00 na yamma. A ranakun Juma’a kuwa, ma’aikata za su fara aiki da karfe 9:00 na safe su kuma tashi da karfe 1:00 na rana, kamar yadda aka saba.” A cewar sanarwar.
Babban Sakataren ya bayyana cewa an yi hakan ne domin baiwa ma’aikatan gwamnati damar shiryawa azumin Ramadan da kuma gudanar da ibadu cikin sauki a wannan wata mai alfarma.
“An yi fatan cewa ma’aikatan gwamnati za su yi amfani da wannan lokaci don yin addu’o’i domin samun shiriya da albarka ga jiharmu,” in ji shi.
Alhaji Muhammad Dagaceri ya kara da cewa ana sa ran ma’aikatan za su yi amfani da lokacin azumi wajen yin addu’o’in zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki ga jihar da kasa baki daya.
END/ USMAN MZ
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
