Labarai
Majalisar ‘Yan Jairda Ta Kano Ta Kaddamar Da Kwamitin Zabe
Majalisar kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya reshen jihar Kano ta kaddamar da kwamitin tantance mutane biyar domin shirya zaben jihar.
An zabo mambobin ne a wani taron gaggawa da aka gudanar a cibiyar ‘yan jarida ta NUJ da ke Kano.
Da yake jawabi a wajen taron shugaban Kungiyar na jiha Kwamared Abbas Ibrahim ya bayyana cewa majalisar ta zabo mambobin kwamitin a tsanake bisa amincinsu.
Kwamitin yana karkashin jagorancin Salisu Babangida daga ma’aikatar yada labarai, Ali Sidi Sharfai na ARTV a matsayin Sakatare.
Sauran sun hada da Abdussalam Na’iya Gwammaja na gidan rediyon Kano da Wasila Ladan ta gidan rediyon Najeriya Pyramid FM da Elizabeth Yila Lamido ta NTA ta Kano a matsayin mambobin kwamitin.
KHADIJAH ALIYU/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
