Connect with us

Labarai

Limamin Pangu Gari Ya Nemi Gwamnan Neja Ya Sanya Baki Kan Rikicin Fili A Yankin

Published

on

An yi kira ga Gwamna Mohammed Umar Bago na jihar Neja da ya sanya baki kan rikicin fili mai fadin sama da hektar saba’in da biyar da ake zargin Hakimin Tegina da ke karamar hukumar Rafi ya kwace daga hannun mamallakinsa a Pangu Gari.

 

Babban Limamin Pangu Gari, Alhaji Umar Musa Danladi ne ya yi wannan kiran yayin da yake zantawa da manema labarai  a Minna, inda ya bayyana cewa hakan yana da muhimmanci matuka,  domin dakile  rikicin da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin.

 

Alhaji Umar Musa Danladi ya bayyana cewa ya gaji filin gonar ne daga mahaifinsa wanda ya rasu kusan shekaru goma da suka gabata, kuma yana da burin barin filin ga ‘ya’yansa su gada.

 

Babban Limamin ya bayyana cewa  wata kotun Shari’a da ke yankin  ta shiga tsakaninsa da wani mutum da ya gina shago a cikin filin, haka kuma ya ci nasara a wata kara da ke dauke da lamba SC/Teg/Cr_25/2024 da ya shigar kan  Hakimin Tegina da wasu mutum bakwai a bara.

 

A cewarsa, ci gaba da cin zarafin da Hakimin Tegina, Alhaji Garba Bako ke yi masa, wani abu ne da ke nuna raina kotu, wanda ya kamata a dauki mataki cikin gaggawa domin samar da zaman lafiya mai dorewa bisa ka’idojin adalci, da gaskiya da gudanar da aiki da nagarta da gwamnatin Gwamna Mohammed Umar Bago ke tsayawa a kai.

 

Sai dai ya zargi Hakimin Tegina, Alhaji Garba Bako, da cewa ya bayar da wani yanki na filin gonar nasa ga wasu manoma domin su noma, tare da umartar jami’an tsaro su kama Babban Limamin Pangu Gari da duk wani dan uwansa da aka gani a filin gonar.

 

Alhaji Musa Umar Danladi ya kuma nemi Sarkin Kagara, Alhaji Attahiru Gunna na biyu wanda ya bayyana a matsayin masoyin zaman lafiya, da ya kara shiga tsakani a rikicin filin gonar domin ya samun abin da ya ce mallakinsa ne na hakika.

 

Ya kuma bukaci ‘yan uwansa su ci gaba da kasancewa cikin zaman lafiya tare da jiran amsa mai kyau da shiga tsakani daga bakin Gwamnan Jihar Neja da kuma Sarkin Kagara, wadanda ya bayyana a matsayin mutane masu gaskiya da adalci akan aikinsu.

 

Daga Aliyu Lawa

 

 

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara