Labarai
Jihar Kano Za Ta Hada Gwiwa Da FMBN Don Samar Da Gidaje Masu Saukin Kudi
Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana aniyarta na ci gaba da hadin gwiwa da Bankin Lamunin Gidaje na Tarayya (Federal Mortgage Bank of Nigeria – FMBN) domin shawo kan matsalar karancin gidaje a jihar.
Gwamnan Jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya bayyana hakan yayin wata ganawa da Babban Daraktan bankin Alhaji Shehu Usman Osidi a ofishinsa.
Gwamna Yusuf ya bayyana muhimmancin wannan hadin gwiwa, yana mai jaddada Kano a matsayin jiha ta biyu mafi yawan jama’a a Najeriya, inda adadin mutanenta ke kara karuwa cikin sauri.
“Kano tana daga sahun gaba wajen ci gaba, kuma samar da gidaje na daga cikin muhimman ginshikai na wannan ci gaba. Akwai bukatar samar da gidaje masu araha domin inganta rayuwar jama’a.” In ji Gwamnan.
A nasa bangaren, Alhaji Shehu Usman Osidi, Manajan Darakta na FMBN, ya bayyana manufar bankin a matsayin taimaka wa ‘yan Najeriya, musamman masu karamin karfi da matsakaicin albashi, wajen samun gidaje masu inganci da saukin kudi.
Ya yabawa gwamnatin Jihar Kano bisa dawo da kanta cikin tsarin Asusun Kasa na Gidaje (National Housing Fund – NHF), yana mai bayyana hakan a matsayin shaida ta shugabanci nagari da jajircewar inganta jin dadin ma’aikata.
Osidi ya bayyana cewa FMBN na da wasu ayyukan rukunin gidaje guda 10 a Kano da suka kai kimanin Naira biliyan 6.8, da nufin rage gibin gidaje da ake fuskanta a jihar.
Ya kuma bayyana shirye-shiryen bankin na kara zurfafa hadin gwiwa da gwamnatin Kano domin cimma burinsu na bai daya.
“Jihar Kano ta koma tsarin NHF a watan Janairun 2025, bayan janyewa tun shekarar 2002. Wannan hadin gwiwa zai taimaka wajen samar da mafita ta gidaje ga ma’aikata tare da inganta walwalarsu,” inji Osidi.
Daga Abdullahi Jalaluddeen
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
