Ilimi
Jihar Kano Ta Samar Da Wani Salo Na Bunkasa Ilmin Addinin Musulunci A Jihar
Gwamnatin jihar Kano ta dauki wani gagarumin mataki na bunkasa ilimin addinin musulunci a jihar ta hanyar hada hannu da kungiyar Agaji ta Musulunci da ke Birtaniya, wato Muslim Charity For United Kingdom a turance.
Wannan haɗin gwiwar na nufin tallafa wa makarantun Islamiyya da kayayyakin koyon ilimi na zamani, da sauransu.
A cewar daraktan wayar da kan jama’a na ma’aikatar ilimi ta jihar Kano, Balarabe Abdullahi Kiru, wannan shiri ya yi daidai da kokarin da gwamnati ke yi na karfafa fannin ilimi.
Haɗin gwiwar zai magance matsalolin da ke addabar ilimin addinin Islama, da tabbatar da cewa makarantun Islamiyya sun sami tallafin da ya dace don samu ingantaccen yanayin karatu da koyarwa.
Ya yi nuni da cewa, Kwamishinan Ilimi na Jihar, Dakta Ali Haruna Makoda, ya bayyana fatan cewa, wannan hadin gwiwa zai inganta ilimin addinin Musulunci, musamman a tsarin makarantun Islamiyya.
Ya ce, shirin zai mayar da hankali ne wajen samar da kayayyakin koyo na zamani domin inganta kwazon dalibai.
Da take jawabi a madadin tawagar, shugabar kungiyar agaji ta addininMusuluncida ke Birtaniya, Dr. Samira Abubakar Abdullahi, ta bayyana cewa kungiyar na aiki tukuru a Najeriya domin tallafawa harkokin ilimi da kiwon lafiya.
Ta bayyana cewa gudummawar da suke bayarwa sun hada da shirye-shiryen gyara makarantu, ayyukan ci gaban ilimi, da ayyukan kiwon lafiya.
“Mun zo ma’aikatar don tattaunawa kan bangarorin haɗin gwiwa da kuma yi wa kwamishina bayani game da ayyukanmu,” inji ta.
Kungiyar agajin tana aiki tukuru a Najeriya don tallafawa ayyukan ilimi da kiwon lafiya.
Daga Khadija Aliyu
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
