Kasuwanci
Gwamnatin Kano Za Ta Yi Aiki Da Kasar Holland Akan Aikin Gona

Gwamna Yusuf Ya Yi Haɗin gwiwa da Gwamnatin Ƙasar Netherland Ba ta Kan Tsaron Abinci, Sauyin Yanayi
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya nemi kasar Netherland ta ba da goyon bayan diflomasiyya domin habaka noma da rage tasirin sauyin yanayi a jihar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana shirin kulla huldar diflomasiyya da gwamnatin kasar Holland, a lokacin da ya karbi bakuncin Ms Eva De Wit, Sakatariyar a Ofishin Jakadancin Netherland a Najeriya.
Gwamna Yusuf ya jaddada tasirin da Holland dake dashi a kan noma da sauyin yanayi a Turai.
Yayin da yake sanar da tawagar kasar Holland matakin da ya dauka game da alkaluman shan muggan kwayoyi da suka gada daga gwamnatin da ta shude, Gwamna Yusuf ya ce an bude cibiyoyin koyar da sana’o’i 24 domin samun kwarin guiwar matasa, su dogara da kansu.
Yusuf ya kara da cewa gwamnatin sa ta kuma gyara halayen wasu matasa kusan 713 da suka tsunduma kansu cikin ayyukan ‘yan daba ta hanyar hadin gwiwa da ‘yan sandan Najeriya domin dakile tashe-tashen hankula a jihar.
A nata bangaren, Ms De Wit wadda ita ma ta samu rakiyar Shugaban Ofishin Jakadancin, Hukumar Kula da ‘yan gudun Hijira ta Duniya, Mista Laurent De Boeck, ta yi alkawarin hada kai da gwamnatin jihar Kano a fannonin inganta rayuwar matasa, samar da abinci da kuma sauyin yanayi.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
