Ilimi
Gwamnatin Jigawa Ta Raba Katin Duba Sakamakon Jarabawa Kyauta Ga Ɗalibai
Gwamnatin Jihar Jigawa ta raba katin duba sakamakon jarabawa ga ɗalibai sama da dubu shida da ɗari biyar da suka kammala makarantun sakandaren Larabci da suka yi nasarar rubuta jarabawar NBAIS ta shekarar 2025 a jihar.
Shugaban Hukumar Ilimin Addinin Musulunci ta Jihar, Dakta Mubarak Abdulwahab Hassan ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Dutse, babban birnin jihar.
A cewarsa, dukkan ɗaliban aji na ƙarshe na makarantun sakandaren Larabci na gwamnati da suka amfana da wannan tallafi sun kammala rubuta jarabawar NBAIS makon da ya gabata, kuma suna jiran sakamakon.
Ya ce wannan tallafi na daga cikin ɗawainiyar da gwamnatin Gwamna Umar Namadi ke yi wajen taimaka wa ɗaliban aji na ƙarshe na sakandaren Larabci domin duba sakamakon nasu cikin lokaci, musamman ga waɗanda ke da niyyar ci gaba da karatu.
Dakta Mubarak Abdulwahab ya ƙara da cewa tun bayan zuwan wannan gwamnati, hukumar ilimin addinin Musulunci ta samu kulawa sosai daga gwamnati, musamman a fannin gyaran makarantu, katange makarantun, ƙirƙirar ƙarin makarantun sakandaren Larabci, da inganta matsayin ilimin addinin Musulunci a makarantun sakandare da sauran fannoni.
Saboda haka, Shugaban Hukumar ya roƙi malamai da shugabannin makarantun sakandaren Larabci a jihar su mayar da martani kan wannan kyauta ta hanyar ƙara himma wajen gudanar da ayyukansu domin cimma nasarorin da ake buri.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai24 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
