Connect with us

Kasuwanci

Gwamnan Jigawa Ya Taya Al’umma Murnar Samun ‘Yancin Kai

Published

on

Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa, ya taya gwamnati da al’ummar Nijeriya murnar cika shekaru 65 da samun ‘yancin kai, inda ya bayyana ranar a matsayin abin tunawa da hadin kai, juriya, sadaukarwa da suka gina kasar.

 

A sakonsa na fatan alheri, Gwamna Namadi ya ce bikin ba wai kawai lokacin yin tunani ne kan irin gwagwarmayar da iyayen da suka kafa kasar suka yi ba, har ma wata dama ce ta sabunta sadaukarwar hadin gwiwa don samar da zaman lafiya, ci gaba, da wadata.

 

“A yau, muna bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ‘yancin kai cikin alfahari da godiya. Wannan ranar tana tunatar da mu sadaukarwar da jaruman mu suka yi a baya, wadanda hangen nesa da jajircewarsu suka kafa tushen kasarmu mai kauna. A matsayinmu na al’umma, dole ne mu ci gaba da tabbatar da akidar hadin kai, adalci, da yiwa bil’adama hidima,” in ji gwamnan.

 

Malam Umar Namadi ya bayyana cewa, duk da kalubalen da Najeriya ke fuskanta, Najeriya na ci gaba da samun ci gaba a karkashin jagorancin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, wanda manufofinsa ke da nasaba da karfafa tattalin arziki, inganta tsaro, da samar da damammaki ga ‘yan kasa.

 

A cewarsa, gwamnatinsa ta dukufa wajen ganin ta kara kaimi ga kokarin gwamnatin tarayya ta hanyar baiwa al’ummarmu fifiko, zuba jari a fannin noma, ilimi, kiwon lafiya, samar da ababen more rayuwa, da samar da damammaki ga matasa da mata.

 

“Tare, za mu gina kasa mai karfi da kuma ba da gudummawa ga daukakar Najeriya.”

 

Namadi ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci gaba da kasancewa da hadin kai da kuma fata, yana mai jaddada cewa bambancin al’ummar kasa ne tushen karfi maimakon rarrabuwa.

 

Ya yi kira ga ‘yan kasa da su ci gaba da marawa manufofi da shirye-shiryen gwamnati goyon baya domin samun ci gaba mai dorewa.

 

“Yayin da muke daga tutarmu mai kore da fari a yau, bari mu tuna cewa alhakin gina Najeriya mai ci gaba ya rataya a kan mu baki daya. Tare da hadin kai, imani, da azama, za mu shawo kan kalubalen mu, mu cika burinmu na kasa mai girma”.

 

USMAN MZ/Dutse

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara