Labarai
Gwamantin Nijar ta ƙara albashi mafi ƙanƙanta ga ma’aikata
Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da yin ƙarin albashi mafi ƙanƙanta ga ma’aikata daga cfa 30,000 zuwa cfa 42,000, wanda ya yi daidai da naira 108,780 a Najeriya.
Wannan ƙarin albashi na daga cikin matakan gwamnatin domin inganta rayuwar ma’aikata da ƙarfafa su wajen gudanar da ayyukansu na yau da kullum, kamar yadda gwamnatin ta sanar.
Majalisar Ministocin gwamnatin ce ta ɗauki wannan mataki a taron da ta gudanar jiya Laraba, inda kuma minsitocin suka tattauna hanyoyin da za a tabbatar da cewa ƙarin albashin zai shafi dukkan ma’aikatan gwamnati ba tare da rarrabewa ba.
Wannan mataki ya zo ne bayan da gwamnatin ta lura da ƙaruwar farashin kayan abinci da sauran kayan masarufi a ƙasar.
Gwamnatin ta bayyana cewa wannan ƙarin albashi zai taimaka wajen rage wahalhalu da ma’aikata ke fuskanta, musamman wajen biyan bukatun yau da kullum kamar abinci, sufuri, da kuma ilimin yara.
-
Labarai6 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Labarai4 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Fasaha5 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai4 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai5 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai4 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai4 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
-
Labarai4 days ago2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro
