Ilimi
Ana nuna damuwa akan karancin kayan gwajin HIV a Taraba
Kungiyoyin farar hula masu yaki da zazzabin cizon sauro, rigakafi da abinci mai gina jiki (ACOMIN), reshen jihar Taraba, ta koka kan matsalar karancin kayan gwajin cutar kanjamau a jihar.
Shugaban kungiyar na jiha, Alhaji Muhammad Danburam ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyarar wayar da kan hukumar yaki da cutar kanjamau ta Taraba (TACA), ofishin kula da magunguna masu muhimmanci, da gidauniyar REDAID Nigeria Foundation., a Jalingo.
Danburam ya bayyana cewa, wani bincike da aka yi kwanan nan a wasu cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko guda 18 a kananan hukumomin Ardo-kola, Bali, da Takum, ya nuna cewa kayan gwajin cutar kanjamau sun kare a cibiyoyin.
“Rashin kayan gwajin zai kawo cikas ga kokarin yaki da yaduwar cutar kanjamau a jihar,” in ji Danburam.
Ya yi kira ga gwamnatin jihar da masu ruwa da tsaki da su dauki matakin gaggawa don magance karancin.
A jawabinsa, Ko’odinetan Sashen Gudanar da Dabaru (LMCU) na Jiha, Pharm. Pinkai Bade, ya bukaci ‘yan kasar da su jajirce wajen tabbatar da samar da wadannan kayyakin tare da bayyana cewa tsarin samar da kayayyaki na da matukar kalubale sakamakon dakatar da tallafin da Amurka ke ba Najeriya.
Ya kuma yi nuni da cewa, Nijeriya ta himmatu wajen ganin an cike gibin da ke tattare da cutar kanjamau da kuma cimma nasarar rigakafin kamuwa da cutar daga uwa zuwa yara (PMTCT) nan da shekarar 2030.
Hukumar kula da fasaha ta REDAID ta Najeriya, Mista Stanley Nfor, da sakataren hukumar yaki da cutar kanjamau ta Taraba (TACA), Mista Bala Zugyeri, sun bayyana cewa, masu hannu da shuni kadai ba za su iya biyan bukatar kayayyakin gwaji da sauran muhimman kayayyaki ba, inda suka jaddada bukatar tallafin gwamnati.
Karshe/Jamila Abba/Wababe
-
Labarai5 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha4 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai4 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai3 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai3 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai3 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai3 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
-
Fasaha3 days agoJigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT
