Labarai
Yadda Athletic Bilbao ta lashe Copa del Rey bayan shekara 40

Athelic Bilbao ta kawo ƙarshen jiran da ta kwashe shekara 40 tana yi domin ta lashe kofin Copa del Rey, bayan nasarar da ta yi kan Mallorca a bugun fenareti a ƙarshen wasan.
Athletic Bilbao ta lashe kofin karo na 24 kuma na farko tun 1984 – lokacin Alex Berenguer da ta yi nasara a bugun fenareti da ci 4-2 a Seville.
An riƙa ihu da tafi bayan nasarar saboda ciwon da ƙungiyar ta ji a baya na zuwa wasan ƙarshe a gasar sau biyu a 2021 kuma tana rashin nasara.
A minti na 21 ne Dani Rodriguez ya ci wa Mallorca kwallo, wato gabanin tafiya hutun rabin lokaci.
A minti na 50 Oihan Sancet ya farkewa Athletic Bilbao.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
