Labarai
Za A Gudanar Da Taron Masana Harkokin Yada Labarai Karo Na 2 A Kano
Daga Khadijah Aliyu
An fara shirye-shirye gudanar da taron shekara-shekara karo na 2 da bikin shigar da sabbin mambobi na Ƙungiyar Masana Harkokin Yada Labarai ta Najeriya (SNB), bayan an kaddamar da Kwamitin Shirya Taron (LOC) a Kano.
An tsara gudanar da taron ne daga ranar 20 zuwa 21 ga watan Nuwamban 2025.
Shugaban Ƙungiyar, Farfesa Umaru A. Pate, ya umarci kwamitin da ya gudanar da aikinsa da himma da jajircewa domin tabbatar da nasarar taron, wanda shi ne irinsa na farko da za a yi a Kano.
Ya bayyana cewa ana sa ran masana sama da 400 da sabbin mambobi daga ciki da wajen jihar za su halarta.
Farfesa Pate ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kano kan jajircewarta wurin inganta aiki da ɗabi’a a harkar yada labarai, yana mai cewa taron zai kasance muhimmiyar dama wacce za ta ƙara ɗaukaka martabar jihar a fagen kafofin yaɗa labarai.
A nasa jawabin, Shugaban LOC, Alhaji Ado Salisu Warawa, ya nuna godiya ga jagorancin ƙungiyar na ƙasa bisa amincewa da kwamitin, yana mai tabbatar da cewa za su gudanar da taron cikin cikakkiyar nasara.
Rel/Khadijah Aliyu
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
