Labarai
’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da makami, tare da ƙwato bindigar AK-47 guda ɗaya da harsasai guda 18, yayin wani samame na bibiyar waɗanda ake zargi a dajin Falgore, da ke Ƙaramar Hukumar Doguwa ta jihar.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Kano.
Ya ce jami’an ’yan sanda na sashen Doguwa, tare da haɗin gwiwar mafarautan sa-kai da aka fi sani da ’Yan Bula, sun gudanar da samamen da misalin ƙarfe 6:30 na safiyar ranar 18 ga Oktoba.
Kiyawa ya bayyana cewa samamen ya biyo bayan wani nasarar aikin tsaro da aka samu a baya, inda aka kashe wasu mutane biyu da ake zargi da zama ’yan bindiga, aka ƙwato kuɗin fansa naira miliyan 10, sannan aka kuɓutar da wani mutum da aka yi garkuwa da shi a dajin Falgore.
Ya bayyana sunan wanda aka kama a matsayin Ibrahim Rabiu, mazaunin ƙauyen Yardoka da ke Ƙaramar Hukumar Kubau ta Jihar Kaduna. Ana zargin sa da hannu a sace Alhaji Kabiru Aliyu, mazaunin ƙauyen Falgore da ke Ƙaramar Hukumar Doguwa.
A cewar sanarwar, mutumin da aka kuɓutar daga hannun masu garkuwa da mutane ya gane wanda ake zargin a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda suka yi garkuwa da shi. Ya ce wanda ake zargin yana gadin sa da dare, yana kawo masa abinci, sannan yana dukansa a lokacin da yake tsare a hannunsu.
Kakakin ’yan sandan ya ce an miƙa wanda ake zargin zuwa sashen binciken manyan laifuffuka na rundunar, musamman sashen yaƙi da garkuwa da mutane, domin gudanar da bincike cikin sirri da kuma ƙoƙarin cafke abokin laifin nasa, wanda ya tsere.
Ya ruwaito Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, yana yaba wa mafarautan ’Yan Bula bisa jarumtaka da jajircewarsu wajen tallafa wa ayyukan tsaro ƙarƙashin Operation Kukan Kura.
Rundunar ta sake jaddada aniyarta ta yaƙi da ayyukan ’yan bindiga, garkuwa da mutane da sauran laifuffuka, tare da kira ga mazauna jihar da su riƙa kai wa hukumomin tsaro sahihan bayanai a kan lokaci.
Fassara: Shafii Abubakar Wababe
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro
