Labarai
Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
Daga BELLO WAKILI, Abuja
Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta samu a Mazabar Tarayya ta Zariya, Jihar Kaduna, Arewa maso Yamma da Najeriya baki ɗaya cikin kwanaki 14 masu zuwa.
Dr. Abbas ya bayyana hakan ne yayin wani taro tsakanin Shugaba Tinubu da ƙungiyar City Boy Movement a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Ya ce rahoton da aka yi wa laƙabi da PBAT Stewardship Account zai ƙunshi ayyukan da gwamnati ta aiwatar da wuraren da aka gudanar da su da kuɗaɗen da aka kashe da kuma matsayin kammala ayyukan, domin bai wa ’yan Najeriya damar tantance sahihancin bayanan.
Shugaban Majalisar ya ba da misali da Asibitin Kwararru na Renewed Hope mai gadaje 100 da ke Zariya, wanda aka buɗe a watan Mayun wannan shekara ƙarƙashin shirin muradun ci gaba mai ɗorewa na gwamnatin, sannan aka miƙa shi ga Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello domin gudanar da ayyukansa.
Ya bayyana cewa asibitin, wanda aka samar wa da ɗakunan tiyata, dakin gwaje-gwaje, na’urar duban ciki da sauran kayan aikin ba da agajin gaggawa, zai inganta samun kiwon lafiya ga mazauna Zariya da yankunan da ke kewaye da ita.
Haka kuma, Shugaban Majalisar ya buƙaci ƙungiyar City Boy Movement da ta samar da tsari guda na bayar da rahoton ayyuka da shirya tarukan tattaunawa da al’umma, tare da bai wa ’yan ƙasa damar tantance ayyukan gwamnati da bayyana ra’ayoyinsu kan yadda ake gudanar da mulki.
Ya roƙi Shugaba Tinubu da ya amince da amfani da tsarin PBAT Stewardship Account a matsayin ma’aunin tantance ayyukan duk masu riƙe da muƙaman siyasa, yana mai jaddada cewa ya kamata a auna shugabanni bisa ayyukan da suke yi wa jama’a, maimakon furucin nuna biyayya kawai.
Dr. Abbas ya ce za a fara aiwatar da wannan shiri daga Zariya, da nufin ƙarfafa gaskiya, riƙon amana da bayyana yadda ake gudanar da mulki.
Fassara: Shafii Abubakar Wababe
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
-
Labarai2 days ago2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro
