Labarai
Ɗan Takarar Gwamnan Accord A Kebbi Ya Yi Alƙawarin Ƙara Albashin Ma’aikata Zuwa N500,000
Daga Sani Haruna Dutsin-ma, B/Kebbi
Ɗan takarar jam’iyyar Accord na kujerar gwamnan Jihar Kebbi, Alhaji Muhammad Sani Abdullahi Bunza, ya yi alƙawarin biyan ma’aikatan gwamnati mafi ƙarancin albashi na naira 500,000 a jihar idan aka zaɓe shi.
Da yake jawabi ga manema labarai a Birnin Kebbi, yayin Taron Tattaunawa da ‘Yan Takara, wanda Ƙungiyar Masu aiko da rahotanno ta Najeriya, reshen Jihar Kebbi, ta shirya, Sani Abdullahi Bunza ya ce albashin da ma’aikatan Najeriya ke karɓa a gida bai yi daidai da halin da ake ciki a ƙasa ba.
Ɗan takarar ya koka kan yadda wasu manufofin gwamnati marasa farin jini suka jefa ma’aikatan gwamnati cikin damuwa da wahalhalu, yana mai cewa irin waɗannan manufofi na ƙara sa ma’aikata zuwa aiki babu karsashi.
Ya tabbatar da cewa ba ya neman kujerar gwamna domin biyan buƙatun kansa ko tara dukiya, sai dai yana takara ne domin ‘yantar da Jihar Kebbi da al’ummarta.
Ɗan takarar gwamnan ya bayyana tsaro a matsayin ɗaya daga cikin manyan abubuwan da zai ba fifiko, yana mai cewa gwamnatocin yanzu a matakai daban-daban ba sa yin isasshen abin da ya kamata wajen kawo ƙarshen ayyukan ‘yan bindiga da satar mutane da sauran laifuffuka a jihar da ma ƙasar baki ɗaya.
Ya lura cewa tsaron ƙasa yana da alaƙa da mutanen da ke kan madafun iko da iyalansu, yana mai cewa babu wani lokaci da aka taɓa sace gwamna ko Sanata ko ɗan Majalisar Wakilai ko minista ko wani daga cikin iyalansu.
Ɗan takarar ya yi alƙawarin tunkarar matsalar tsaro kai tsaye, domin bai wa al’ummar Kebbi fata da zaman lafiya. Ya kuma ce za a ba ɓangaren kiwon lafiya kulawa ta musamman, domin kawo ƙarshen buƙatar ‘yan Najeriya na zuwa ƙasashen waje neman magani.
Saboda haka, ɗan takarar ya yi kira ga masu zaɓe a faɗin Jihar Kebbi da su yi amfani da hikima wajen zaɓensu, tare da kaɗa ƙuri’unsu ga jam’iyyar Accord.
Fassara: Shafii Abubakar Wababe
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
