Labarai
Kano Ta Raba Kayan Koyarwa Ga Ɗaliban Fiye Da 5
Daga Khadijah Aliyu, Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta fara rabon kayan koyarwa ga ɗalibai 5,022 da ke ƙarƙashin Shirin Hanzarta Samar da Ilimin Firamare, wato Accelerated Basic Education Programme (ABEP).
Ƙungiyar Plan International Nigeria ce ke tallafa wa shirin da kuɗaɗen Tarayyar Turai, da nufin sauƙaƙa wa ɗaliban ABEP komawa tsarin ilimi na yau da kullum.
Kwamishinan Ilimi na Jihar Kano, Gwani Dakta Ali Haruna Abubakar Makoda, ne ya ƙaddamar da rabon kayan a Kano.
Ana sa ran kowane ɗalibi da ya amfana zai samu kunshin kayan da ya ƙunshi jakar makaranta, littattafan rubutu da takalmi guda biyu da robar ruwa.
Da yake jawabi a wajen taron, Dakta Makoda ya ce samar da kayan zai ƙara tallafa wa ƙoƙarin gwamnatin jihar na samar da yanayin da ya dace da koyo ga yara masu rauni, tare da ƙarfafa musu gwiwar ci gaba da karatunsu.
Kwamishinan ya jaddada aniyar gwamnatin jihar na tabbatar da cewa babu wani yaro da za a bari a baya wajen samun ilimi.
Ya ce haɗin gwiwa da abokan hulɗar ci gaba na da matuƙar muhimmanci wajen magance ƙalubalen ilimi da kuma faɗaɗa damar samun ilimi ga yara a faɗin jihar.
Dakta Makoda ya buƙaci waɗanda suka amfana da su kula da kayan da aka ba su tare da amfani da su bisa manufar da aka samar da su.
Ya kuma yi kira ga iyaye da masu kula da yara da malamai da shugabannin al’umma da sauran masu ruwa da tsaki da su ci gaba da tallafa wa ɗaliban a duk tsawon lokacin karatunsu.
Kwamishinan ya yaba wa Plan International da hukumomin gwamnati da masu gudanar da Shirin da masu ruwa da tsaki a cikin al’umma da sauran abokan hulɗar ci gaba bisa gudummawar da suke bayarwa wajen aiwatar da shirin.
Shi ma da yake nasa jawabin, Jami’in Plan International a jihar, Alhassan Hamza Hussain, ya ce kayan za su taimaka wajen magance wasu daga cikin muhimman buƙatun waɗanda suka amfana, tare da ƙarfafa musu gwiwar halartar ayyukan koyarwa a kai a kai.
Ya yaba wa Ma’aikatar Ilimi da hukumomin ilimi da al’ummomi da sauran masu ruwa da tsaki bisa gudummawar da suka bayar wajen samun nasarar shirin.
Bisa bayanan shirin, ɗalibai 5,022 da wannan shiri na haɗa su da tsarin ilimi na yau da kullum ya shafa, sun fito ne daga zaɓaɓɓun cibiyoyin koyarwa da ke ƙananan hukumomin Gwale da Kumbotso da Nasarawa.
Daga cikin waɗanda suka amfana, 1,211 sun fito ne daga ƙaramar hukumar Gwale, yayin da 2,643 suka fito daga Kumbotso, sannan 1,168 suka fito daga ƙaramar hukumar Nasarawa.
An tsara Shirin Hanzarta Samar da Ilimin Firamare, ABEP, ne domin samar da damar samun ilimi ga yara da matasa waɗanda suka rasa damar shiga tsarin ilimi na yau da kullum ko kuma aka ware su daga cikinsa.
Fassara; Shafii Abubakar Wababe
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
