Connect with us

Labarai

Kwara PDP Ta Yi Kira Ga INEC Ta Binciki Zargin Shigo Da ‘Yan Kasashen Waje

Published

on

Daga ALI MUHAMMAD RABIU

Jam’iyyar PDP a Jihar Kwara ta yi kira ga Hukumar Zaɓe ta Ƙasa da ta gudanar da bincike kan zargin cewa wasu ‘yan siyasa a jihar na shigo da ‘yan ƙasashen waje da nufin amfani da su wajen tafka magudin zaɓe a babban zaɓen 2027.

Da yake jawabi yayin wani taron horaswa na kwana guda kan shirye-shiryen zaɓe da aka gudanar a Ilorin domin mata sama da 3,000 na PDP daga shiyyoyin sanata uku na jihar, mai taken “Ƙuri’armu, Ƙarfimmu — Mu Tashi Tsaye Tare Don Makomarmu”, Shugaban PDP na jihar, Malam Isa Bawa, ya ce ana zargin an bai wa wasu daga cikin ‘yan ƙasashen wajen katunan zaɓe domin su kaɗa ƙuri’a a babban zaɓen da ke tafe.

Shugaban PDP ya ambaci ƙaramar hukumar Baruten da ke shiyyar Kwara ta Arewa a matsayin ɗaya daga cikin wuraren da ake zargin lamarin ya faru, inda ya buƙaci INEC ta kasance alkalin wasa na gaskiya ta hanyar hukunta waɗanda aka samu da hannu a wannan lamari.

Ya kuma yi kira ga INEC da ta binciki zargin ayyukan wata hukumar gwamnati da ke da alhakin tsara yadda ake manna fastoci da kuma kafa allunan tallace-tallace, yana mai cewa an cire allunan tallace-tallacen ‘yan takarar PDP na babban zaɓen 2027.

Bawa ya kuma buƙaci INEC ta sa ido kan yaɗa ɓatanci tsakanin ‘yan siyasa, ganin cewa kamfen ya fara, tare da ba da shawarar cewa hukumar zaɓen ta shirya muhawara tsakanin ‘yan takara domin su samu damar bayyana wa al’ummar Kwara tsare-tsarensu da manufofinsu ga jihar da al’ummarta.

Ya tabbatar wa matan PDP cewa jam’iyyar adawar za ta kawo sauyi idan ta koma mulki, inda ya danganta nasarar da aka samu a zaɓen baya-bayan nan a Jihar Osun da shigar mata da rawar da suka taka a harkokin zaɓe.

Shugaban ya buƙaci matan da su ɗauki babban zaɓen 2027 da muhimmanci tare da shirya tsaf domin kare ƙuri’unsu.

A nata jawabin, Shugabar Mata ta PDP a Jihar Kwara, Hajiya Aminat Isola, ta ce mata na da muhimmiyar rawa wajen samar da ƙarfin masu zaɓe a duk wani zaɓe mai ‘yanci da adalci da zaman lafiya da sahihanci a kowace dimokuraɗiyya.

Hajiya Isola ta buƙaci matan jihar da su koyi tsarin kaɗa ƙuri’a tun daga tantance masu zaɓe, kaɗa ƙuri’a, ƙirga ƙuri’u da bayyana sakamako a rumfunan zaɓe, har zuwa tattara sakamako a matakin gunduma yayin babban zaɓen 2027.

Fassara: Shafii Abubakar Wababe

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara