Kasuwanci
‘Yan Sandan Kano Sun Kama Mutane 78 Da Ake Zargi Da Safarar Miyagun Kwayoyi
A wani samame na kwanaki hudu na hadin gwiwa na yakar shaye-shayen miyagun kwayoyi da tashe-tashen hankula a kan tituna, rundunar hadin guiwa mai wanzar da zaman lafiya da farfado da matasa ta jihar Kano, ta kama wasu mutane 78 da ake zargi a manyan wuraren da ke jihar.
A wata sanarwar manema labarai da jami’in hulda da jama’a na hukumar NDLEA a Kano Sadiq Mohammad Maigatari ya fitar, ya ce rundunar ta yi aiki tare da hadin gwiwar hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA da kuma rundunar ‘yan sandan Najeriya.
Wannan farmakin dai ya shafi fitattun wuraren da ake aikata miyagun laifuka da suka hada da Mariri Yan’itace, Fagge, Badawa, Masallacin Idi, da Kofar Mata. Sauran wurare kamar su Kwalejin Rumfa, Makabartar Dan’agundi, da Kofar Wambai an kai sumame. Jami’ai sun tabbatar da cewa 60 daga cikin wadanda aka kama suna da alaka kai tsaye da laifukan da suka shafi muggan kwayoyi ko ayyukan ‘yan daba.
Sanarwar ta yi bayanin cewa an gano wasu haramtattun abubuwa yayin da ake share su, wadanda suka hada da wiwi, Diazepam, Exol-5, Pregabalin, maganin roba, da cakudar titinan gida da ake kira “Suck and Die.” Mahukunta sun ce kamun ya nuna yadda ake samun karuwar shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin matasan Kano.
Dokta Yusuf Ibrahim Kofar Mata wanda ya jagoranci aikin, ya ce gwamnati na ci gaba da jajircewa wajen ganin ta kawar da shaye-shayen miyagun kwayoyi da tashe-tashen hankula tsakanin matasa. “Za mu ci gaba da aiki don ganin an gurfanar da wadanda ke da hannu a gaban shari’a tare da magance tushen abubuwan ta hanyar gyarawa da ilimi.”
Kwamandan NDLEA ACGN A.I. Ahmad ya yaba da kokarin da aka yi tare kuma ya bukaci jama’a da su goyi bayan kokarin aiwatar da ayyukan da ake yi.
Ya kuma jaddada mahimmancin shigar da al’umma domin samar da jihar Kano mai zaman lafiya, ba ta da miyagun kwayoyi.
Abdullahi Jalaluddeen/Kano
-
Labarai3 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai4 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai4 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai4 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai3 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai2 days agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai22 hours agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
-
Labarai2 days agoShettima Ya Bukaci ’Yan Najeriya Su Sake Zaben Tinubu A 2027
