Connect with us

Labarai

Man Utd Na Tattaunawa Da Golan PSG, Chelsea Ta Nace Wa Garnacho

Published

on

Manchester United ta soma tattaunawa da Paris St-Germain kan golan Italiya Gianluigi Donnarumma, mai shekara 26, amma Chelsea da Manchester City na cikin masu sha’awar golan. (Telegraph – subscription required, external)

Yayin da ɗanwasan gaba na Sweden Alexander Isak, mai shekara 25, ya amince ya koma LiverpoolNewcastle ta saka ɗanwasan Brazil Rodrigo Muniz, mai shekara 24 cikin lissafinta. (Mail – subscription required, external)

Crystal Palace ta sanar da Arsenal cewa sai ta fara biya aƙalla fam miliyan 35 kafin ta ɗauko Eberechi Eze, daga baya ta cike sauran kuɗin. (Guardian, external)

Palace a shirye take ta biya fam miliyan 27.6 domin ɗauko ɗanwasan baya na Jamus Yann Bisseck, mai shekara 24 daga Inter Milan domin maye gurbin Marc Guehi, da ake alaƙantawa da Liverpool. (Gazzetta dello Sport – in Italian, external)

Chelsea na ci gaba da matsi kan Alejandro Garnacho amma Manchester United na son ta biya ta fam miliyan 40 kan ɗanwasan gaban na Argentina. (Talksport, external)

Lyon ta cimma matsaya tsakaninta da ɗanwasan tsakiya na Liverpool da Ingila Tyler Morton, mai shekara 22, amma kudin da Liverpool ta nema zai iya kawo cikas ga yarjejeniyar. (L’Equipe – in French, external)

AS Roma na nazarin ɗauko ɗanwasan gaba na Wolves Portugal Fabio Silva, mai shekara 23, yayin da kuma take da sha’awar ɗanwasan Argentina da Manchester City mai shekara 19 Claudio Echeverri. (Sky Sports, external)

Matashin ɗanwasan Ingila mai shekara 19 Leo Castledine na shirin zuwa Huddersfield Town a matsayin aro daga Chelsea. (Athletic – subscription required, external)

Ɗanwasan baya na Ingila Rob Holding, mai shekara 29, na shirin barin Crystal Palace domin komawa ƙungiyar Amurka ta Colorado Rapids. (Sky Sports, external)

Middlesbrough ta amince da tayin fam miliyan 20 da Ipswich ta yi kan ɗanwasan Ingila Hayden Hackney, mai shekara 23. (Northern Echo)

Labarai

Labarai1 day ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai6 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara