Labarai
Gwamnatin Taliban Ta Katse Hanyoyin Sadarwa a Ƙasar
Mahukuntan Taliban a Afghanistan sun sanar da rufe dukkanin hanyoyin sadarwa a fadin kasar, makonni bayan da suka fara katse intanet, domin hana abin da suka bayyana a matsayin tabarbarewar tarbiyya.
Wata kungiya mai sa ido kan harkokin yanar gizo ta ce yanzu baki ɗaya ana fama da rashin intanet a kasar.
Wani jami’in Taliban ya ce rufewar za ta ci gaba har sai an bayar da wata sanarwa a nan gaba.
Shugaban Taliban, Hibatullah Akhund-zada, ya bayar da umarnin fara cire wayoyin sadawar dake ƙarkashin kasa na intanet tun a farkon wannan wata.
BBC ta rawaitu cewar kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce ya rasa ji ta hanyoyin sadarwa daga ofishinsa na Kabul, ciki har da ta wayar salula.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
