Connect with us

Kasuwanci

Gwamnatin Kano Ta Jaddada Kudirinta Na Bunkasa Kiwon Dabbobi Da Noma Na Zamani

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta jaddada aniyar ta na inganta kiwon dabbobi da inganta ayyukan noma na zamani a fadin jihar.

 

Kwamishinan noma Dakta Danjuma Mahmud ne ya bayyana haka a yayin taron bita na kwanaki biyu ga ma’aikatan aikin gona da aka gudanar a Kadawa da ke karamar hukumar Garun Malam.

 

 

Dokta Danjuma Mahmud, wanda babban sakatare a ma’aikatar Dr Bashir Sunusi ya wakilta ya ce an shirya taron bitar ne domin wadata ma’aikatan noma dabarun zamani da nufin bunkasa noma da kiyo dabbobi da kuma bunkasa amfanin gona.

 

 

Ya ce ma’aikatan za su gudanar da kwakkwaran horo kan kiwon dabbobi domin ba da damar kiwo na nau’in da za su iya samar da madara da nama mai yawa domin amfanin dan Adam.

 

Ya kuma jaddada cewa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf a kwanakin baya ta dauki daruruwan ma’aikatan aikin gona a matsayin dabarunta na kawo sauyi ga harkar noma da tabbatar da samar da abinci a jihar.

 

A nasa jawabin wani kwararre a fannin noma Malam Gambo Isa ya bayyana cewa horon zai kara habaka kwazon ma’aikatan da ake sa ran za su mika ilimin da sana’o’in da suka samu ga manoma tun daga tushe.

 

 

Ya kuma bukaci mahalarta taron da su tabbatar da cewa alfanun da aka samu horon ya ragu ga manoman yankin domin cimma manufofin da aka sanya a gaba.

 

Wasu daga cikin mahalarta taron sun yi alkawarin yin amfani da ilimin da aka samu yadda ya kamata, musamman wajen inganta kiwon dabbobi da amfanin gona.

 

Horarwar ta kwanaki biyu ta tattaro mahalarta daga dukkan kananan hukumomi 44 na jihar Kano.

 

 

ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara