Labarai
UNILORIN Ta Zama Ta Farko A Najeriya Wajen Ingancin Bincike
Daga Ali Muhammad Rabi’u, Ilorin
Jami’ar Ilorin (UNILORIN) ta zama jami’ar da ta zo ta farko a Najeriya wajen ingancin bincike, bisa sabon jadawalin manyan jami’o’in duniya na Times Higher Education (THE).
A wata sanarwa da Daraktan Harkokin Hulɗa da Jama’a na jami’ar, Mista Kunle Akogun, ya rabawa manema labarai, an ce jami’ar ta samu kashi 69.4 cikin 100, wanda shi ne mafi girman maki da wata jami’ar Najeriya ta samu a wannan fanni a jerin jami’o’in bana.
Sanarwar ta ce an fitar da sakamakon jadawalin ne ranar Laraba, 30 ga Satumba, 2026, a yayin taron World Academic Summit da aka gudanar a Jami’ar Cape Town da ke Afirka ta Kudu.
A cewar sanarwar, jadawalin yana tantance jami’o’i ne bisa ginshiƙai guda biyar, waɗanda suka haɗa da koyarwa da yanayin bincike da ingancin bincike da hulɗar ƙasa da ƙasa da kuma hulɗa da masana’antu.
Sanarwar ta ambato, Farfesa Suleiman Ambali, yana cewa “ingancin bincike shi ne fannin da UNILORIN ta fi ƙarfi a kai,” inda ya ce jami’ar na da burin mayar da wannan nasara zuwa ƙarin karɓuwa a matakin duniya, tare da kokarin shiga rukunin jami’o’in da ke tsakanin matsayi na 801 zuwa 1000.
Ya ce ingancin bincike yana da kaso 30 cikin 100 na jimillar maki, kuma yana auna yadda masana a sassa daban-daban na duniya ke amfani da binciken da jami’a ta gudanar tare da ambatonsa a ayyukansu na ilimi.
Da yake mayarda jawabi kan wannan nasara, Shugaban Jami’ar, Farfesa Wahab Egbewole, SAN, ya ce sakamakon ba hatsari ba ne, sai dai sakamakon shekaru na aiki tuƙuru da jajircewa da bin ƙa’idojin binciken ilimi da malamai suka yi, musamman waɗanda ke wallafa ayyukan bincike da masana a duniya ke karantawa da ambatonsu.
Shugaban Jami’ar ya gode wa dukkan malaman jami’a da masu bincike da masu kula da ɗaliban digiri na biyu da kuma ɗalibai, waɗanda gudummawar ayyukansu ta taimaka wajen samun wannan matsayi mai kyau.
Fassara: Shafii Abubakar Wababe
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
