Labarai
Nasarawa A Shekara 30: Sule Ya Jaddada Muhimmancin Zaman Lafiya
Daga Aliyu Muraki, Lafia
Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya ce zaman lafiya da haɗin kai su ne ginshiƙan ci gaba da jawo masu zuba jari da bunƙasa tattalin arzikin jihar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a bikin al’adu na jihar da aka shirya domin murnar cika shekaru 30 da kafuwar Jihar Nasarawa.
Gwamna Sule ya ce makomar tattalin arzikin Nasarawa, musamman a fannin ma’adanai masu daraja, ta dogara ne kan zaman lafiya da kwanciyar hankalin jihar. Ya ƙara da cewa daga cikin muhimman ma’adanai guda bakwai da ake da su a Najeriya, dukkan su ana samunsu a Jihar Nasarawa.
Ya ce: “Muna da babbar masana’antar sarrafa lithium a Afirka a nan Nasarawa, saboda masu zuba jari sun ga akwai zaman lafiya.”
Gwamnan ya ce jihar ta samu nasarar jawo masu zuba jari waɗanda ke haƙo ma’adanai tare da sarrafa su a cikin jihar, yana mai danganta wannan ci gaba da zaman lafiya da kyakkyawar zaman tare tsakanin al’ummomin jihar.
Da yake magana kan rikicin siyasa da kan kunno kai kafin zaɓe, Gwamna Sule ya yi kira ga ‘yan siyasa da magoya bayansu da su kasance masu haƙuri da juna yayin yakin neman zaɓe.
Gwamna Abdullahi Sule ya kuma gode wa sarakunan gargajiya, musamman Mai Martaba Sarkin Lafia da baƙi daga ƙasar Ireland da Cibiyar Hulɗa da Jama’a ta Najeriya da Hukumar Kula da Yawon Buɗe Ido ta Ƙasa bisa halartar bikin al’adun jihar.
Wakilinmu da ke Lafia ya ruwaito cewa jerin gwanon bikin al’adun, wanda ya fara daga ƙofar birnin ya kuma ƙare a filin Lafia, ya haɗa ƙabilu da ƙungiyoyin al’adu daban-daban waɗanda suka baje kolin al’adunsu masu ɗimbin yawa, abin da ya kayatar da mahalarta da masu kallo.
Fassara: Shafii Abubakar Wababe
-
Labarai4 days agoHukumar Alhazai Ta Jigawa Ta Bayyana Alhininta Bisa Rasuwar Suleiman Usman
-
Fasaha3 days agoNASENI Ta Ƙarfafa Horar da Sana’o’i da Fasahar Jiragen Sama Marasa Matuki a Kaduna
-
Labarai3 days agoNSCDC Ta Kama Wanda Ake Zargi Da Safarar Mutane A Zamfara
-
Labarai2 days agoGwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya
-
Labarai2 days agoGwamna Uba Sani Ya Ce Bunƙasa Ƙwarewa Na Da Muhimmanci Ga Farfaɗo Da Tattalin Arziki
-
Labarai2 days agoGwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga
-
Labarai2 days agoTajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14
-
Labarai2 days ago’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano
