Connect with us

Labarai

APC Ta Yi Watsi Da Zargin Maidoki Na Kamawa Da Tuhumar ‘Yan ADC Ba Bisa Ka’ida Ba

Published

on

Daga Sani Haruna, Kebbi

Jam’iyyar APC reshen Jihar Kebbi, ta yi watsi da zargin Sanata Garba Musa Maidoki na jam’iyyar ADC, cewa kamawa da sarewa da gurfanar da wasu daga cikin mambobi da magoya bayan ADC da aka yi, na da nasaba da siyasa.

Sakataren Yaɗa Labarai na APC a jihar, Alhaji Isah Abubakar Assalafi, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a Birnin Kebbi, inda yake mayar da martani kan taron manema labaran da Sanata Maidoki ya gudanar kwanan nan.

Ya bayyana zargin muzgunawa mutane bisa dalilan siyasa a matsayin babban batu da ya kamata a tabbatar da shi ta hanyar sahihan hujjoji, ba wai kalaman siyasa kawai ba, yana mai jaddada cewa babu wani mutum ko jam’iyyar siyasa da ya kamata a ɗaukaka shi sama da sahihin bincike da kuma bin doka.

Assalafi ya ƙalubalanci ADC da ta gabatar da hujjar da ke danganta Gwamnatin Jihar Kebbi da zargin kama mutane ba bisa ƙa’ida ba, musamman duk wata hujja da ke nuna cewa gwamnati ta bayar da umarni ga jami’an tsaro da su kai wa mutane hari saboda kasancewarsu mambobin wata jam’iyya.

Ya ce idan akwai hujjar rashin da’a daga ‘yan sanda da amfani da iko ba bisa ƙa’ida ba ko kuma tsoma bakin siyasa a cikin ayyukan jami’an tsaro, ya kamata a miƙa irin waɗannan hujjoji ga hukumomin da suka dace domin gudanar da bincike, maimakon kafa irin wannan zargi ta hanyar kalaman da ake yi a kafafen yaɗa labarai.

Assalafi ya kuma gargadi Sanata Maidoki da kada ya yi ƙoƙarin tsara wa jami’an tsaro yadda za su gudanar da ayyukan da doka ta ɗora musu, yana mai cewa ya kamata a bar ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro su gudanar da ayyukansu cikin ƙwarewa da bin doka, domin kare lafiyar jama’a da tabbatar da zaman lafiya da oda.

A cewarsa, gwamnati na ci gaba da samar wa hukumomin tsaro motocin aiki da kayan aiki da sauran abubuwan da suke buƙata domin ƙarfafa musu damar tunkarar matsalolin tsaro yadda ya kamata, musamman a yankunan da ke cikin haɗari da wuraren noma.

Ya jaddada cewa gwamnatin jihar ta himmatu wajen ƙarfafa tsarin tsaro da kuma tallafa wa matakan da suka dace da doka domin tabbatar da zaman lafiya da kare rayukan jama’a da kuma hana aikata laifuka.

Saboda haka, Assalafi ya yi kira ga ADC da sauran ‘yan siyasa da su mutunta bin doka tare da guje wa mayar da halaltattun ayyukan jami’an tsaro na tabbatar da doka batun siyasa.

Ya ce APC ba za ta goyi bayan muzgunawa kowane ɗan ƙasa saboda dalilan siyasa ba, haka kuma ba za ta amince da amfani da kasancewa a wata jam’iyya a matsayin kariya daga halastaccen bincike ko gurfanarwa bisa doka ba.

Fassara: Shafii Abubakar Wababe

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara