Connect with us

Ilimi

Maniyyata 51,447 Ne Za Su Sauke Farali A Aikin Hajjin Bana – NAHCON

Published

on

Hukumar Alhazai ta Najeriya, ta ce aƙalla maniyyatan Najeriya 51,447 ne za su sauke farali a aikin Hajjin bana a ƙasar Saudiyya.

Shugaban hukumar, Malam Jalal Arabi, ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da aka gudanar ranar Juma’a a Abuja.

Arabi ya ce hukumar na tsare-tsare wajen ganin ta gudanar da aikin Hajji cikin nasara, ko da kuwa za a fuskanci kalubale.

Ya nanata cewa Msulman Najeriya za su yi aikin Hajjin 2024 a adadin da babu wanda ya taɓa tunani.

“Shirye-shiryen Hajjin bana na ɗaya daga cikin mafi wahala da aka taɓa gani,” in ji shi.

Ya ce a baya, an samu lokaci mai yawa na yin shirin da ya kamata, amma a wannan karon, Saudiyya ba ta ba su isasshen lokaci ba.

Malam Arabi ya ce gwamnatin tarayya ta shiga taimaka ta hanyoyi da dama, musamman ma ɓullo da wasu tsare-tsare na tallafa wa hukumar domin tabbatar da cewa al’amura su tafi yadda ya dace.

Ma’aikatar aikin Hajji da Umrah ta Saudiyya ta ware wa Najeriya kujeru 95,000 domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2024.

Labarai

Labarai14 hours ago

Jam’iyyar PDP Ta Kauracewa Zaben Kananan Hukumomi A Jihar Neja

Jam’iyyar PDP a Jihar Nasarawa ta ce ba za ta yi takara a zaben  kananan hukumomi da za a gudanar...

Labarai17 hours ago

Gobara: ‘Yan Majalisar Zamfara Sun Jajantawa Shugaban Majalisar

‘Yan majalisar dokokin jihar Zamfara sun bayyana kaduwarsa dangane da gobarar da ta tashi a gidan shugaban majalisar, Bilyaminu Ismail...

Labarai1 day ago

Isra’ila Ta Lalata Wani Masallaci A Harin Lebanon

Dakarun tsaron Isra’ila sun lalata wani wuri mai girman gaske a Lebanon, ciki har da wani masallaci mai nisan kilomita...

Labarai1 day ago

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Mutane Da Dama A Zamfara

Wasu da ake zargin ƴan bindiga sun toshe babbar hanyar Gusau zuwa Funtua mai cike da cunkoso tare da yin...

Kasuwanci1 day ago

Farashin Kiret Din Kwai Zai Iya Kai 10,000 – Masu kiwon kaji

Ƙungiyar masu kiwon kaji ta Najeriya ta ce nan ba da jimawa ba kiret ɗin kwai zai iya kai naira...

Labarai1 day ago

Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Jigawa Ta Raba Tallafi A Karamar Hukumar Gwaram

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Jigawa (SEMA) ta raba tallafin fiye da naira miliyan takwas da dubu dari tara...

Ilimi3 days ago

Gwamna Namadi Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar Tsangaya Ta Jihar Jigawa

Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya amince da nadin Dakta Abubakar Maje Hamisu a matsayin babban sakataren zartarwa na...

Labarai3 days ago

An Gaza Cimma Matsaya Tsakanin IPMAN Da NNPCL

Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya (IPMAN) ta nuna damuwarta bisa yiwuwar fuskantar matsalar karancin mai duk...

Labarai3 days ago

Gwamna Radda Ya Ba Da Gudunmawar Dala Dubu 10 Ga Jamhuriyar Nijar

Biyo bayan rushewar masallacin garin Damagaram na Jamhuriyar Nijar, Gwamna Dikko Umar Radda na jihar Katsina ya bayar da gudunmawar...

Labarai3 days ago

Shugaba Tinubu Ya Yi Ta’aziyya Ga Mele Kyari Kan Rasuwar ‘Yarsa

  Shugaba Bola Tinubu ya yi ta’aziyya ga Babban Darakta na Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPCL), Mista Mele Kolo...

Mafi Shahara