Algeria ta ce zata aike da wani kudiri MDD na neman a kawo karshen wannan kisa.
Gwamnatin Washington ta ce tana bibiyan abubuwan da ke faruwa, duk da dai ta nuna goyan-bayan Isra’ila a Rafah, inda take cewa babban farmakin fatatakar ‘yan ta’adda ne.
Sai dai kuma a wani bangaren tace akwai takaici ganin yadda hare-haren jiya Talata suka lakume karin rayuwa fararan-hula a sansanin ‘yan gudun hijira da ke yankin Rafah.
Isra’ila dai ta ce ba ita ta kai wannan harin ba.