Connect with us

Labarai

Zanga Zanga: Gwamnati Ta Baiwa Matasa Tabbacin Daukan Bukatun Su Da Mahimmanci

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta bukaci matasan da suke da niyyan yin Zanga zanga a kasar nan dasu dakata saboda tana yin duk maiyuyuwan domin biya musu bukatunsu.

Ministan Labarai Muhammad Idris ne ya sanar da haka ga manema labarai a fadar shugaban kasa Sailin dayake tsokaci kan batun zanga zanga da wasu matasan kasan nan suke sonyi.

Ministan labarai Muhammad idris yace shugaba tinubu ya dukufa wajen sauraren korafe korafen matasan.

Ya kuma baiwa matasan tabbacin cewa yaji duk bukatan nasu kuma ya daukesu da mahimmanci.

Ministan na labarai ya roki matasan dasu dakata da zanga zanga sannan su jira suga abunda gwamnati zatayi.

Ya kumayi nuni da wasu tsare tsare da gwamnati tayi domin kawo sauki ga al’umma musamman amincewa da Majalisar dokokin kasan nan tayi da mafi karancin albashi batare da bata lokaci ba

Har ila yau Ministan ya kara da cewa sun kuma tattauna da shugaban kasan kan batutuwan da suka shafi kafofin yada labarai mallakan gwamnatin tarayya ta yadda zasuyi aiki yadda yakamata.

A kakokarin da gwamnatin takeyi domin kawo sauki ga al’umma yayi waiwayen wasu ababen da gwamntin tarayya ta amince dasu wa’yanda suka hada da baiwa jahohi shinkafa domin su rabawa al’umma batare da shamaki bad a kuma shirin baiwa dalibai rance domin kara karatu

Bello Wakili

Labarai

Labarai1 day ago

Ziyarar Shugaba Tinubu Zuwa China Ta Yi Nasara

  Ziyarar Shugaba Tinubu zuwa China Ta Yi Nasara, da kuma Shaida Wa ‘Yan Najeriya Mazauna China, Yi Alkawarin don...

Labarai1 day ago

Sabon Tsarin Albashi: Majalisar Kano Ta Amince da Karin Kasafin Naira Biliyan 99

Majalisar Dokokin Kano ta amince da ƙarin kasafin kudi na N99bn da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike mata domin...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Musanta Jita-Jitar Bayar Da Kudi Ga ‘Yan Ta’adda

  Gwamnatin Jihar Zamfara tayi watsi da jita-jitar da ke yawo cewar tana shirin bayar da kudi ga wasu sanannun...

Labarai2 days ago

Shugaba Tinubu Ya Dauki Matakan Gaggawa Don Wadata Man Fetur da Farashinsa

  Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Ɗauki Matakai Masu Ƙarfi don Magance Samuwar Man Fetur da Farashi a Faɗin Najeriya A...

Labarai2 days ago

Tinubu Ya Nemi Hadin Gwiwar Afirka da China Don Bunkasa Tattalin Arziki

  Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a ci gaba da hadin kai tsakanin Afrika da Sin, yana mai...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya ta Amince da Tsare-tsare Don Yakar Rashin Abinci Mai Gina Jiki

  Daga: Bello Wakili Ministan Tsare-tsare na Lafiya da Walwala ta Jama’a na kasa, Muhammad Ali Pate, ya jaddada muhimmancin...

Labarai3 days ago

ACF Ta Ce Babban Kalubalen Arewa Yanzu Shi Ne Rashin Tsaro

Kungiyar Tuntubar Arewa, wato Arewa Consultative Forum (ACF) ta ce a halin yanzu, batun da ya fi damun al’ummar arewacin...

Labarai3 days ago

Hukumar NOA Ta Yabawa Majalisar Jihar Nasarawa Wajen Samarda Dokoki Masu Amfani ga Jama’a

Hukumar Wayar da Kan Jama’a da Fadakarwa ta Kasa (NOA) ta yaba wa Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa bisa ga kafa...

Kasuwanci3 days ago

Shugaba Tinubu Ya Gana da Firayim Ministan Sin, Ya Ce Afirka Na Da Damar Zuba Jari da Haɓaka

  Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ce Afrika na da manyan damammaki wajen zuba jari, ci gaba, da haɓaka tare...

Labarai3 days ago

Tinubu Ya Jajantawa Jihar Yobe Kan Rashe-Rashen Rayukan da Aka Yi a Tarmuwa

  Shugaba Bola Tinubu ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Yobe kan rashin rayukan da aka yi a Mafa a...

Mafi Shahara