Labarai
Putin Ya Gargaɗi Koriya ta Kudu Game Da Bai Wa Ukraine Makamai
Shugaban Vladimir Putin ya gargaɗi Koriya ta Kudu kan abin da ya kira “babban kuskure” idan ta sake ta aika wa Ukraine makamai a yaƙin da take yi da Rashar.
Kalaman nasa na zuwa ne bayan Seoul ta ce tana duba yiwuwar yin hakan a matsayin martani ga yarjejeniyar tsaro da Rashar ta ƙulla da Koriya ta Arewa domin taimaka wa juna idan wata ƙasa ta kai wa ɗayarsu hari.
Moscow “za ta…[ɗauki] matakin da ba lallai ya yi wa shugabannin Koriya ta Kudu daɗi ba idan ta bai wa Ukraine makamai”, kamar yadda Mista Putin ya shaida wa manema labarai ranar Alhamis.
Shugaban na Rasha na magana ne a Vietnam jim kaɗan bayan ziyarar da ya kai Pyongyang babban birnin Koriya ta Arewa, inda suka saka hannu kan yarjejeniyar tare da Shugaba Kim Jong Un.
Putin ya kuma yi gargaɗin cewa Rasha za ta bai wa Koriya ta Arewa makamai idan Amurka da ƙawayenta suka ci gaba da bai wa Ukraine makamai.
“Waɗanda suke bayar da waɗannan makaman suna tunanin cewa ba yaƙi suke yi da mu ba. Na faɗa cewa baya ga Koriya ta Arewa, muna da ‘yancin tura makamai zuwa sassan duniya,” a cewar Putin.
Tun da farko Koriya ta Kudu ta yi tir da yarjejniyar da ƙasashen suka ƙulla a matsayin wata barazana ga tsaron ƙasarta, har ma mai ba da shawara kan tsaro Chang Ho-jin ya ce ƙasarsa na shirin “duba bai wa Ukraine makamai”.
Yayin da Koriya ta Kudu ta bai wa Ukraine tallafin kayayyaki da kuma was kayan aikin soji, zuwa yanzu ba ta ba ta makaman yaƙi ba sakamakon tsarinta na ƙin bai wa wata ƙasa makamai matuƙar tana cikin yaƙi.
Yayin ziyarar, Mista Kim ya bayyana “cikakken goyon bayansa” ga mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine. Akwai hujjoji masu ƙwari da ke nuna tuni Rashar ta fara amfani da makaman Koriyar a kan
-
Ilimi6 days ago
Gwamna Namadi Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar Tsangaya Ta Jihar Jigawa
-
Labarai7 days ago
Kashim Shettima Ya Kaddamar da Majalisar Shawara ta Kasa Kan Tsaro
-
Labarai7 days ago
Shugaba Tinubu Ya Yi Ta’aziyya Ga Mele Kyari Kan Rasuwar ‘Yarsa
-
Labarai7 days ago
An Gaza Cimma Matsaya Tsakanin IPMAN Da NNPCL
-
Labarai5 days ago
Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Jigawa Ta Raba Tallafi A Karamar Hukumar Gwaram
-
Labarai7 days ago
Gwamna Radda Ya Ba Da Gudunmawar Dala Dubu 10 Ga Jamhuriyar Nijar
-
Labarai4 days ago
Jam’iyyar PDP Ta Kauracewa Zaben Kananan Hukumomi A Jihar Nasarawa
-
Labarai4 days ago
Gobara: ‘Yan Majalisar Zamfara Sun Jajantawa Shugaban Majalisar