Ilimi
Mai Martaba Sarkin Gumel Ya Jaddada Kudirinsa Na Tallafawa Makarantun Tsangaya Da Islamiyya
Mai Martaba Sarkin Gumel da ke Jihar Jigawa, Alhaji Ahmad Muhammad Sani ya sake jaddada kudirinsa na ci gaba da tallafawa makarantun tsangaya da na islamiya domin samar da mahaddata Alqur’ani a fadin masarautarsa.
Mai Martaban ya bayyana hakan yayin bikin yaye mahaddata Alqur’ani 27 da makarantar marigayi Malam Habu Gade ta gudanar karo na 12 a garin Gumel.
Ya ce masarautarsa tana maraba da makarantun tsangaya da na islamiya domin ci gaba da hidimtawa Alqur’ani mai tsarki.
Mai Martaba Sarkin wanda ya sami wakilcin Sa’in Gumel, Alhaji Sani Abdullahi ya bukaci iyaye da su tabbatar ‘Yayansu na zuwa makarantun mahammadiya da na zamani domin samun ilmi.
Tun da farko a nasa jawabin, shugaban makarantar Malam Lawan Abubakar Gade ya ce wannan shine karo na 12 da makarantar ta yaye mahaddata Alqur’ani maza da mata tun kafuwarta a shekarar 1970.
Yana mai mika godiygrsa ga Gwamnatin jihar Jigawa bisa sanya makarantar a cikin tsarin makarantun Tsangaya tare da godewa Mai martaba sarki bisa goyon baya da ya ke bawa makarantar.
A jawabinsa a madadin iyayen yara Malam Hassan Magaji ya ce za su ci gaba da sa ido akan zuwa ‘yayansu makaranta akan lokaci.
Usman Mohammed Zaria
-
Kasuwanci7 days ago
PDP Katsina Ta Zabi Sabbin Shugabanni
-
Labarai6 days ago
Kamfanin Mai Na Kasa Na Fuskantar Matsalolin Kudaden Samar Da Man Fetur
-
Labarai6 days ago
Gwamna Lawal Ya Yi Sabon Nadi Ga Hukumar Asusun Kula Da Harkokin Tsaro
-
Kasuwanci6 days ago
Gwamnatin Tarayya Ta Fara Gina Rukunan Gidaje 500 A Kano
-
Labarai5 days ago
Shugaba Bola Tinubu Ya Jajantawa Iyalan Yar’Adua Bisa Rasuwar Hajiya Dada
-
Labarai7 days ago
Ku Gaggauta Kammala Ayukkan Da Ke Hannun Ku A Arewa Maso Gabas
-
Labarai3 days ago
ACF Ta Ce Babban Kalubalen Arewa Yanzu Shi Ne Rashin Tsaro
-
Labarai6 days ago
APC Ta Lashe Dukkan Kujerun Kansiloli Da Kansiloli A Kebbi