Connect with us

Labarai

Gwamnatin Tarayya Ta Kaddamar Da Shirin Bunkasa Harkar Noma A Yobe

Published

on

­Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da shirin karfafa aikin noma a jihar Yobe.

Shirin wanda ya hada da samar da injinan noma da kayan aiki, wani shiri ne na inganta samar da abinci, da samar da ayyukan yi, da habaka tattalin arzikin Najeriya.

Shugaba Tinubu wanda mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta, ya bayyana muhimmiyar rawar da noma ke takawa wajen ci gaban kasa, inda ya ce, “Abinci shi ne ginshikin kwanciyar hankali a rayuwar kowace al’umma”. Ya jaddada bukatar tallafawa tare da karfafawa manoma gwiwa don cimma manyan manufofin gwamnati.

 

Shirin wanda ke da nufin zamanantar da fannin noma, na da bada tallafi na musamman ga jihar Yobe da suka hada dasamar da  kananan rijiyoyin ban ruwa, famfuna masu amfani da hasken rana, sinadaran  noma, injinan janareta, da takin zamani. An yi hakan ne domin saukaka noman rani, da rage dogaro da noman damina.

Shugaba Tinubu ya kuma yi tsokaci kan matsalolin tsaro, inda ya ba da tabbacin daukar matakan tabbatar yin noma cikin kwanciyar hankali a fadin kasar nan.

Mataimakin shugaban Shettima wanda ya ziyarci Sarkin Damaturu, ya mika sakon jinjinawa daga shugaba Tinubu kan irin gudunmawar da al’ummar jihar Yobe ke bayarwa, sannan ya yaba da nasarorin da Gwamna Mai Mala Buni ya samu a harkar noma.

 

A nasa jawabin, Gwamna Buni ya jaddada goyon bayan jihar ga gwamnatin Tinubu tare da bayyana wasu tsare-tsare na farfado da harkar noma da suka hada da hadin gwiwa da kungiyoyi irin su gidauniyar Bill and Melinda Gates. Ya kuma bayyana kafa cibiyoyin raya dabbobi da farfado da shirin noman rani na Lava.

Taron kaddamar da aikin ya kunshi rarraba kayayyakin amfanin gona iri-iri da suka hada da taraktoci na Zoom Lion 100, motocin IMC Double Cabin 10, da famfunan ban ruwa masu amfani da hasken rana guda 4,202 da dai sauransu.

 

Wadanda suka halarci taron sun hada da Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo, mataimakan shugabannin jam’iyyar APC na kasa Hon. Ali Bukar Dalori da Cif Emma Eneukwu, Sanata Ahmed Lawan, da sauran manyan baki.

Wannan shiri dai ya nuna wani gagarumin ci gaba a kokarin Najeriya na samun wadatar abinci da habaka tattalin arziki ta hanyar noma.

 

Daga Bello Wakili

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Labarai1 day ago

Ziyarar Shugaba Tinubu Zuwa China Ta Yi Nasara

  Ziyarar Shugaba Tinubu zuwa China Ta Yi Nasara, da kuma Shaida Wa ‘Yan Najeriya Mazauna China, Yi Alkawarin don...

Labarai1 day ago

Sabon Tsarin Albashi: Majalisar Kano Ta Amince da Karin Kasafin Naira Biliyan 99

Majalisar Dokokin Kano ta amince da ƙarin kasafin kudi na N99bn da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike mata domin...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Musanta Jita-Jitar Bayar Da Kudi Ga ‘Yan Ta’adda

  Gwamnatin Jihar Zamfara tayi watsi da jita-jitar da ke yawo cewar tana shirin bayar da kudi ga wasu sanannun...

Labarai2 days ago

Shugaba Tinubu Ya Dauki Matakan Gaggawa Don Wadata Man Fetur da Farashinsa

  Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Ɗauki Matakai Masu Ƙarfi don Magance Samuwar Man Fetur da Farashi a Faɗin Najeriya A...

Labarai2 days ago

Tinubu Ya Nemi Hadin Gwiwar Afirka da China Don Bunkasa Tattalin Arziki

  Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a ci gaba da hadin kai tsakanin Afrika da Sin, yana mai...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya ta Amince da Tsare-tsare Don Yakar Rashin Abinci Mai Gina Jiki

  Daga: Bello Wakili Ministan Tsare-tsare na Lafiya da Walwala ta Jama’a na kasa, Muhammad Ali Pate, ya jaddada muhimmancin...

Labarai3 days ago

ACF Ta Ce Babban Kalubalen Arewa Yanzu Shi Ne Rashin Tsaro

Kungiyar Tuntubar Arewa, wato Arewa Consultative Forum (ACF) ta ce a halin yanzu, batun da ya fi damun al’ummar arewacin...

Labarai3 days ago

Hukumar NOA Ta Yabawa Majalisar Jihar Nasarawa Wajen Samarda Dokoki Masu Amfani ga Jama’a

Hukumar Wayar da Kan Jama’a da Fadakarwa ta Kasa (NOA) ta yaba wa Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa bisa ga kafa...

Kasuwanci3 days ago

Shugaba Tinubu Ya Gana da Firayim Ministan Sin, Ya Ce Afirka Na Da Damar Zuba Jari da Haɓaka

  Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ce Afrika na da manyan damammaki wajen zuba jari, ci gaba, da haɓaka tare...

Labarai3 days ago

Tinubu Ya Jajantawa Jihar Yobe Kan Rashe-Rashen Rayukan da Aka Yi a Tarmuwa

  Shugaba Bola Tinubu ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Yobe kan rashin rayukan da aka yi a Mafa a...

Mafi Shahara