Ilimi
Gwamnati Za Ta Yiwa Madatsar Ruwan Alau Garanbawul A Barno
Gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na yin garambawul tare da tabbatar da madatsar ruwa ta Alau da ke Maiduguri a jihar Borno ba ta sake zama hadari ga al’umma ba.
Ministan albarkatun ruwa da tsaftar mahalli, Joseph Utsev ya ba da wannan tabbacin a lokacin da ya jagoranci kwamitin ma’aikatun kasar a ziyarar tantance madatsar ruwa.
Ziyarar ta kwamitin ta biyo bayan mummunar ambaliyar da aka yi a ranar 10 ga watan Satumba, wadda ta yi sanadin salwantar rayuka da dama, tare da raba sama da mutane miliyan guda, tare da lalata muhimman ababen more rayuwa da filayen noma na biliyoyin naira a sassan jihar.
Ministan wanda Daraktan madatsun ruwa a ma’aikatar, Malam Aliyu Dala ya wakilta, ya bayyana cewa, wurin da ya rufta, wanda ya kai ga ambaliya a Maiduguri da kewaye, shi ne babban abin da aka fi mayar da hankali wajen tantancewar.
Utsev ya jaddada cewa, kwamitin zai yi nazari kan yanayin da dam din ke ciki, da kuma tasirinsa na zamantakewa da muhalli ga al’ummomin yankin, inda ya kara da cewa, manufar ita ce samar da mafita na gajeren lokaci da na dogon lokaci don hana bala’o’i a nan gaba.
Ministan ya tabbatar da aniyar gwamnati na kammala ayyukan kwamitin kafin damina mai zuwa.
Shugaban kwamatin da ke kula da madatsar ruwan Alau na jihar Borno, Alhaji Mohammed Sanda ne ya jagoranci tawagar zagayen gine-ginen madatsar ruwan.
Ya kara da cewa mazauna Maiduguri sun dogara ne da ruwa daga madatsar ruwan domin amfanin yau da kullum, yana mai alakanta ambaliya da aka yi a baya-bayan nan da ruwan sama mai yawa, tare da toshe hanyoyin ruwa, da karkatar da ruwa zuwa tafkin Alau.
Kwamitin ma’aikatun ya hada da kwararru daga ma’aikatun albarkatun ruwa da tsaftar muhalli, ayyuka da gidaje, muhalli, kasafin kudi, da kuma wakilai daga ofishin mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa, da kungiyar Injiniyoyi ta Najeriya (NSE), da kuma majalisar. Tsarin Injiniya a Najeriya (COREN).
Cov/Dauda/Wababe
-
Ilimi6 days ago
Gwamna Namadi Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar Tsangaya Ta Jihar Jigawa
-
Labarai6 days ago
Kashim Shettima Ya Kaddamar da Majalisar Shawara ta Kasa Kan Tsaro
-
Labarai6 days ago
Shugaba Tinubu Ya Yi Ta’aziyya Ga Mele Kyari Kan Rasuwar ‘Yarsa
-
Labarai4 days ago
Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Jigawa Ta Raba Tallafi A Karamar Hukumar Gwaram
-
Labarai6 days ago
An Gaza Cimma Matsaya Tsakanin IPMAN Da NNPCL
-
Labarai6 days ago
Gwamna Radda Ya Ba Da Gudunmawar Dala Dubu 10 Ga Jamhuriyar Nijar
-
Labarai4 days ago
Jam’iyyar PDP Ta Kauracewa Zaben Kananan Hukumomi A Jihar Nasarawa
-
Labarai4 days ago
Gobara: ‘Yan Majalisar Zamfara Sun Jajantawa Shugaban Majalisar