Connect with us

Labaran Gida

Wani Fitaccen Mai taimakon Al’umma ya Kawo Ziyara gidan Rediyon Tarayya na Kaduna

Published

on

Shugaban Kamfanonin Amuz Global Ventures Alhaji Magaji Dan- Aljannah ya ziyarci gidan Rediyon Tarayya na Kaduna,domin ganin yadda suke gudanar ayyukan su, da kuma tattaunawa ga me da irin kaluban da suke fuskanta.

 

Ayayin ziyarar Alhaji Magaji Dan- Aljannah,yayi alkawarin taimakawa,gidan Rediyon musamman yadda yaga cewa itace babbar kafar sadarwa wajen  illimantarwa da kokarin hada kan Al’ummar Arewacin Kasar nan.

Har’ila yau Jigon kanfanin na Amuz Global Ventures ya Jinjinawa Mahukunta da Ma’aikatan gidan Rediyon, musamman yadda yaga suna bakin kokarin su dan tafiyar da tashar gaba.

 

Alhaji Magaji Dan- Aljannah yayi matukar nuna damuwarshi ganin yadda Hukumar lantarki ta KEDCO ke kawo wa tashar gidan Rediyon kudin wuta da yake wuce kima, idan yace lalle zai taimaka wajen ganin an warware matsalar wutan lantarki da ake yawan fuskanta a tashar.

A yayin Jawabin Shugaban gidan Rediyon Tarayya na Kaduna Mallan Buhari Auwalu ya godewa Alhaji Magaji Dan- Aljannah dan ziyarar daya kawo wa gidan Rediyon, ganin cewa wannan Tasha na daya daga cikin mahimman abubuwan da Marigayi Sardaunan Sokoto ya kawo wa Arewacin Najeriya Dan ganin cigaban ta yankin.

Mallan Buhari Auwalu ya yabawa Alhaji Magaji Dan- Aljannah ganin cewa ya dauki alkawarin taimakawa gidan Rediyon wajen warware wasu matsalolin da suke fuskanta.

 

Ziyarar ya sami tattaunawa da Mahukunta na gidan Rediyon Tarayya na Kaduna, musamman wajen ganin irin rawar ganin da Attajirai da kafafen gwamnati ka iya haduwa su kawo wajen ganin su warware wasu matsalolin Kasa.

CovAbubakar Hamza.

 

Labarai

Labarai1 day ago

Ziyarar Shugaba Tinubu Zuwa China Ta Yi Nasara

  Ziyarar Shugaba Tinubu zuwa China Ta Yi Nasara, da kuma Shaida Wa ‘Yan Najeriya Mazauna China, Yi Alkawarin don...

Labarai2 days ago

Sabon Tsarin Albashi: Majalisar Kano Ta Amince da Karin Kasafin Naira Biliyan 99

Majalisar Dokokin Kano ta amince da ƙarin kasafin kudi na N99bn da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike mata domin...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Musanta Jita-Jitar Bayar Da Kudi Ga ‘Yan Ta’adda

  Gwamnatin Jihar Zamfara tayi watsi da jita-jitar da ke yawo cewar tana shirin bayar da kudi ga wasu sanannun...

Labarai2 days ago

Shugaba Tinubu Ya Dauki Matakan Gaggawa Don Wadata Man Fetur da Farashinsa

  Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Ɗauki Matakai Masu Ƙarfi don Magance Samuwar Man Fetur da Farashi a Faɗin Najeriya A...

Labarai2 days ago

Tinubu Ya Nemi Hadin Gwiwar Afirka da China Don Bunkasa Tattalin Arziki

  Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a ci gaba da hadin kai tsakanin Afrika da Sin, yana mai...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya ta Amince da Tsare-tsare Don Yakar Rashin Abinci Mai Gina Jiki

  Daga: Bello Wakili Ministan Tsare-tsare na Lafiya da Walwala ta Jama’a na kasa, Muhammad Ali Pate, ya jaddada muhimmancin...

Labarai3 days ago

ACF Ta Ce Babban Kalubalen Arewa Yanzu Shi Ne Rashin Tsaro

Kungiyar Tuntubar Arewa, wato Arewa Consultative Forum (ACF) ta ce a halin yanzu, batun da ya fi damun al’ummar arewacin...

Labarai3 days ago

Hukumar NOA Ta Yabawa Majalisar Jihar Nasarawa Wajen Samarda Dokoki Masu Amfani ga Jama’a

Hukumar Wayar da Kan Jama’a da Fadakarwa ta Kasa (NOA) ta yaba wa Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa bisa ga kafa...

Kasuwanci4 days ago

Shugaba Tinubu Ya Gana da Firayim Ministan Sin, Ya Ce Afirka Na Da Damar Zuba Jari da Haɓaka

  Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ce Afrika na da manyan damammaki wajen zuba jari, ci gaba, da haɓaka tare...

Labarai4 days ago

Tinubu Ya Jajantawa Jihar Yobe Kan Rashe-Rashen Rayukan da Aka Yi a Tarmuwa

  Shugaba Bola Tinubu ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Yobe kan rashin rayukan da aka yi a Mafa a...

Mafi Shahara