Connect with us

Labarai

Sanatocin Arewa Sun Jinjinawa Tinubu Bisa Amincewa Da Kafa Hukumar Raya Arewa Maso Yamma

Published

on

Kungiyar Sanatocin Arewa ta yabawa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa rattaba hannu kan kudirin hukumar raya yankin Arewa maso Yamma ta zama doka

Wasikar yabon wacce shugaban kungiyar Abdulaziz ‘Yar’adua ya sanya wa hannu, ta ce wannan gagarumar nasara da aka samu ta kara sanya kwarin gwiwa kan kudirin gwamnati na bunkasa al’umma musamman yankin Arewa maso Yamma.

Ya kara da cewa  hangen nesa irin  na Shugaba Tinubu ya karfafa gwiwar al’umma na inganta tsaro a shiyyar Arewa maso Yamma da ke fama da matsalar  tsaro a ‘yan shekarun nan.

Abdulaziz  ‘Yaradua ya kuma bayyana cewa kafa hukumar wani muhimmin mataki ne na magance matsalolin da suke haifar da rashin tsaro, da suka hada da talauci, da  rashin aikin yi, da rashin samun  damammaki da sauransu.

Shugaban kungiyar sanatocin ya kuma bayyana cewa, “mayar da hankali ga hukumar wajen magance matsalar karancin abinci da bunkasa noma, zai yi tasiri kai tsaye ga rayuwar al’ummar mu, wadanda suke  fafutuka wajen samun kayayyakin masarufi“.

Kokarin da gwamnatinka ke yi na farfado da fannin noma na tabbatar da samar da abinci, zai kuma samar da ayyukan yi da bunkasar tattalin arziki“.

Ya bayyana jin dadinsa da cewa hukumar za ta ba da fifiko wajen magance matsalar yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin, duba da yadda ilimi shi ne ginshikin ci gaba, kuma kudurin da shugaba Tinubu ya yi na ganin cewa dukkan yaran Nijeriya sun samu ilimi mai inganci  abin a yaba ne.

Haka kuma, farfado da sana’ar auduga a yankin Arewa, wadda a da ta kasance bangaren ci gaban tattalin arziki, zai yi matukar tasiri ga tattalin arziki, kuma tabbas za a iya samar da ayyukan yi, da samar da arziki, da bunkasar masana’antu“.

A wani labarin kuma  mataimakin majalisar dattawa Barau Jibrin ya yabawa shugaban kasa Bola Tinubu bisa amincewa da kudirin kafa hukumar.

Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya yi imanin cewa hukumar za ta taimaka wajen samar da ci gaba a fadin jihohi bakwai na shiyyar.

Ya kuma ba da tabbacin cewa masu ruwa da tsaki a shiyyar, za su hada kai don ganin hukumar ta ci gaba da aiki da manufar kafa ta, don haka ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da marawa shugaba Bola Tinubu baya domin cigaban kasa.

 

Bashir Meyere

Labarai

Ilimi18 hours ago

Gwamnati Za Ta Yiwa Madatsar Ruwan Alau Garanbawul A Barno

Gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na yin garambawul tare da tabbatar da madatsar ruwa ta Alau da ke Maiduguri a...

Fasaha19 hours ago

Majalisar Zartaswar Jihar Jigawa Ta Fitar Kudaden Tallafin Karatu

Majalisar zartaswa ta jihar Jigawa ta amince da kudi sama da naira miliyan dari bakwai da casa’in da takwas domin...

Labarai19 hours ago

Kungiyar Tsoffin Manyan Sakatarorin Zamfara Ta Sami Kyautar Mota

Gwamna Lawal Ya Ba Da Kyautar Mota Ga Ƙungiyar Tsaffin Manyan Sakatarorin Da Suka Yi Ritaya A Zamfara Gwamnan Jihar...

Labarai20 hours ago

An Tsinci Gawar Tauraron Mawakan One Direction Liam Payne

Liam Payne, ɗaya daga cikin mawaƙa a tawagar One Direction, ya mutu a Argentina bayan ya faɗo daga hawa na...

Labarai20 hours ago

Gwamnatin Tarayya Ta Jajantawa Wadanda Fashear Tankar Mai Ta Shafa A Jigawa

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bayyana matukar alhininsa dangane da mummunan fashewar tankar da ta afku a garin Majiya...

Ilimi20 hours ago

Hukumar Hisbah Ta Ziyarci Majalisar Dokokin Kano

Majalisar dokokin jihar Kano ta ce ta kuduri aniyar tabbatar da ingantattun tsare-tsare na walwala ga ma’aikatan Hisba domin tabbatar...

Fasaha20 hours ago

Za A Fafata A Gasar Tseren Doki Ta Masarautar Gwandu

Ana sa ran al’ummomin duniya daga Hadaddiyar Daular Larabawa da kasashen yammacin Afirka za su halarci gasar tseren doki na...

Kasuwanci20 hours ago

Gwamnan Niger Ya Kaddamar Da Shirin Kula da Lafiyar ‘Yan Fansho Da Tsofaffi

Gwamna Mohammed Umaru Bago na jihar Neja ya kaddamar da kunshin inshorar lafiya, wani shiri da aka tsara don samar...

Labarai21 hours ago

Kamala Harris Ta Yi Alkawarin Sauya Salon Mulkin Amurka Idan Ta Lashe Zabe

Ƴar takarar shugabancin Amurka a jam’iyyar Democrat, Kamala Harris, ta yi alƙawarin sauya salo daga irin kamun ludayin shugaba Joe...

Labarai4 days ago

Jam’iyyar PDP Ta Kauracewa Zaben Kananan Hukumomi A Jihar Nasarawa

Jam’iyyar PDP a Jihar Nasarawa ta ce ba za ta yi takara a zaben  kananan hukumomi da za a gudanar...

Mafi Shahara