Connect with us

Ilimi

Mata Da Marasa Galihu Za Su Amfana Da Tallafin Naira Miliyan 110 A Jihar Kabi

Published

on

Asusun kula da kananan Yara na Majalisar Dunkin Duniya UNICEF, ya shirya bada na Naira miliyan 110 ga matalauta dubu 10,200 domin ba su damar samun ayyukan kiwon lafiya kyauta a jihar Kebbi.

 

Shugaban ofishin UNICEF na Sokoto, Michael Juma, wanda ya bayyana hakan a wata ziyarar ban girma da ya kai wa Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya kuma ba da tabbacin cewa UNICEF ta himmatu wajen taimaka wa matalauta da mata da yara marasa galihu domin samun ayyukan kiwon lafiya musamman mazauna karkara.

 

Yayin da yake nuna godiyar UNICEF ga Gwamna Idris da ya jagoranci gwamnatinsa kan aiwatar da wasu tsare-tsare na yara da mata don ci gaban jama’a baki daya, ya yaba wa Gwamnan bisa amincewa da aiwatar da wasu manufofi, dokoki, da tsare-tsare kan lokaci da za su tabbatar da ci gaban al’umma a jihar.

 

Hukumar ta amince da kafa kotuna guda biyu a cikin babban birnin jihar, Birnin Kebbi, wadanda za su gabatar da duk wasu shari’o’in da suka shafi take hakkin yara musamman cin zarafin mata da kuma bayar da tabbacin UNICEF na bayar da goyon baya wajen tabbatar da kotunan sun cika ka’idojin da aka shimfida na yara a duniya.

 

 

A nasa jawabin, Gwamna Nasir Idris, ya godewa UNICEF bisa kokarin da take yi wa al’ummar jihar ta hanyar aiwatar da shirye-shirye daban-daban da nufin inganta rayuwar mata da yara musamman a fannin kiwon lafiya, ilimi, abinci mai gina jiki, da manufofin zamantakewa.

 

Abdullahi Tukur/Wababe

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Ilimi18 hours ago

Gwamnati Za Ta Yiwa Madatsar Ruwan Alau Garanbawul A Barno

Gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na yin garambawul tare da tabbatar da madatsar ruwa ta Alau da ke Maiduguri a...

Fasaha18 hours ago

Majalisar Zartaswar Jihar Jigawa Ta Fitar Kudaden Tallafin Karatu

Majalisar zartaswa ta jihar Jigawa ta amince da kudi sama da naira miliyan dari bakwai da casa’in da takwas domin...

Labarai19 hours ago

Kungiyar Tsoffin Manyan Sakatarorin Zamfara Ta Sami Kyautar Mota

Gwamna Lawal Ya Ba Da Kyautar Mota Ga Ƙungiyar Tsaffin Manyan Sakatarorin Da Suka Yi Ritaya A Zamfara Gwamnan Jihar...

Labarai19 hours ago

An Tsinci Gawar Tauraron Mawakan One Direction Liam Payne

Liam Payne, ɗaya daga cikin mawaƙa a tawagar One Direction, ya mutu a Argentina bayan ya faɗo daga hawa na...

Labarai19 hours ago

Gwamnatin Tarayya Ta Jajantawa Wadanda Fashear Tankar Mai Ta Shafa A Jigawa

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bayyana matukar alhininsa dangane da mummunan fashewar tankar da ta afku a garin Majiya...

Ilimi19 hours ago

Hukumar Hisbah Ta Ziyarci Majalisar Dokokin Kano

Majalisar dokokin jihar Kano ta ce ta kuduri aniyar tabbatar da ingantattun tsare-tsare na walwala ga ma’aikatan Hisba domin tabbatar...

Fasaha20 hours ago

Za A Fafata A Gasar Tseren Doki Ta Masarautar Gwandu

Ana sa ran al’ummomin duniya daga Hadaddiyar Daular Larabawa da kasashen yammacin Afirka za su halarci gasar tseren doki na...

Kasuwanci20 hours ago

Gwamnan Niger Ya Kaddamar Da Shirin Kula da Lafiyar ‘Yan Fansho Da Tsofaffi

Gwamna Mohammed Umaru Bago na jihar Neja ya kaddamar da kunshin inshorar lafiya, wani shiri da aka tsara don samar...

Labarai20 hours ago

Kamala Harris Ta Yi Alkawarin Sauya Salon Mulkin Amurka Idan Ta Lashe Zabe

Ƴar takarar shugabancin Amurka a jam’iyyar Democrat, Kamala Harris, ta yi alƙawarin sauya salo daga irin kamun ludayin shugaba Joe...

Labarai4 days ago

Jam’iyyar PDP Ta Kauracewa Zaben Kananan Hukumomi A Jihar Nasarawa

Jam’iyyar PDP a Jihar Nasarawa ta ce ba za ta yi takara a zaben  kananan hukumomi da za a gudanar...

Mafi Shahara