Connect with us

Fasaha

Majalisar Zartaswar Jihar Jigawa Ta Fitar Kudaden Tallafin Karatu

Published

on

Majalisar zartaswa ta jihar Jigawa ta amince da kudi sama da naira miliyan dari bakwai da casa’in da takwas domin siyan kayayyakin abinci na agajin gaggawa na SEMA da kuma shirye-shiryen kayan agaji da shiga tsakani kamar yadda ma’aikatar ayyuka ta musamman ta gabatar.

 

Kwamishinan Yada Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na Jihar Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron majalisar wanda Gwamna Umar Namadi ya jagoranta a gidan gwamnati dake Dutse.

 

A cewarsa, kayayyakin sun hada da buhunan masara da gero 6000, katon spaghetti 12,000 da kuma buhunan Garri 2000.

 

Alhaji Sagir Musa Ahmed ya ce a bisa kokarin da gwamnatin jihar ke yi na inganta harkar ilimi a jihar, majalisar ta amince da kashe sama da naira miliyan 740 domin bayar da kwangilar gina ajujuwa, dakunan gwaje-gwaje, bandakuna, dakunan gudanarwa, dakunan gwaje-gwaje na ICT. da kuma taron bita a wasu zababbun makarantu a fadin jihar.

 

Ya yi nuni da cewa makarantun sun hada da GDSTC Kafin Hausa da Babura, CGSSS- Roni & Jahun, GDSTC Gumel, Kanya Babba, GDSSS Ringim, Dutse da Hadejia.

 

Sagir ya ci gaba da bayyana cewa, majalisar ta kuma amince da biyan alawus alawus na kudi sama da naira miliyan 624 na sabbin dalibai 14,269 da aka tantance kuma suke karatu a jami’ar Sule Lamido kafin Hausa, da Kwalejin horasda Malamai ta Gumel, da Kwalejin kimiyya da fasaha ta jiha da ke Dutse da Hadejia da kuma Kwalejin Horasda malamai ta Hadejia da Kwalejin Nazarin Shari’a ta Ringim

 

USMAN MZ/Wababe

Labarai

Ilimi20 hours ago

Gwamnati Za Ta Yiwa Madatsar Ruwan Alau Garanbawul A Barno

Gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na yin garambawul tare da tabbatar da madatsar ruwa ta Alau da ke Maiduguri a...

Fasaha20 hours ago

Majalisar Zartaswar Jihar Jigawa Ta Fitar Kudaden Tallafin Karatu

Majalisar zartaswa ta jihar Jigawa ta amince da kudi sama da naira miliyan dari bakwai da casa’in da takwas domin...

Labarai21 hours ago

Kungiyar Tsoffin Manyan Sakatarorin Zamfara Ta Sami Kyautar Mota

Gwamna Lawal Ya Ba Da Kyautar Mota Ga Ƙungiyar Tsaffin Manyan Sakatarorin Da Suka Yi Ritaya A Zamfara Gwamnan Jihar...

Labarai21 hours ago

An Tsinci Gawar Tauraron Mawakan One Direction Liam Payne

Liam Payne, ɗaya daga cikin mawaƙa a tawagar One Direction, ya mutu a Argentina bayan ya faɗo daga hawa na...

Labarai22 hours ago

Gwamnatin Tarayya Ta Jajantawa Wadanda Fashear Tankar Mai Ta Shafa A Jigawa

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bayyana matukar alhininsa dangane da mummunan fashewar tankar da ta afku a garin Majiya...

Ilimi22 hours ago

Hukumar Hisbah Ta Ziyarci Majalisar Dokokin Kano

Majalisar dokokin jihar Kano ta ce ta kuduri aniyar tabbatar da ingantattun tsare-tsare na walwala ga ma’aikatan Hisba domin tabbatar...

Fasaha22 hours ago

Za A Fafata A Gasar Tseren Doki Ta Masarautar Gwandu

Ana sa ran al’ummomin duniya daga Hadaddiyar Daular Larabawa da kasashen yammacin Afirka za su halarci gasar tseren doki na...

Kasuwanci22 hours ago

Gwamnan Niger Ya Kaddamar Da Shirin Kula da Lafiyar ‘Yan Fansho Da Tsofaffi

Gwamna Mohammed Umaru Bago na jihar Neja ya kaddamar da kunshin inshorar lafiya, wani shiri da aka tsara don samar...

Labarai23 hours ago

Kamala Harris Ta Yi Alkawarin Sauya Salon Mulkin Amurka Idan Ta Lashe Zabe

Ƴar takarar shugabancin Amurka a jam’iyyar Democrat, Kamala Harris, ta yi alƙawarin sauya salo daga irin kamun ludayin shugaba Joe...

Labarai4 days ago

Jam’iyyar PDP Ta Kauracewa Zaben Kananan Hukumomi A Jihar Nasarawa

Jam’iyyar PDP a Jihar Nasarawa ta ce ba za ta yi takara a zaben  kananan hukumomi da za a gudanar...

Mafi Shahara