Kasuwanci
Kwastan Sun Yi Wawan Kamu Tsakanin Kogi Da Neja
Hukumar Kwastam reshen Neja Kogi ta kama wasu buhunan tabar wiwi guda dari biyu da tamanin da uku a wani samame da ta kai jihar Kogi.
Shugaban rundunar ‘yan sandan jihar, Mista Pascal Chbuoke ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Minna, jihar Neja.
Mista Pascal Chbuoke ya bayyana cewa, jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Kogi da ke sintiri tare da bibiyar wasu bayannan sirri sun yi nasarar kama wata mota kirar Honda Accord mai lamba FKJ 678 DJ kuma takardu sun tabbatar da an biya kudin harajin sama da naira miliyan biyar na motar da ke kan babbar hanyar Lokoja Abuja, sai dai bisa zargin tana ɗauke da haramtattun abubuwa ya sa aka bincika kuma aka yi dace.
A cewarsa direban ya bar motar ne yayin da jami’ansa suka gudanar da bincike mai zurfi inda ya gudu zuwa daji saboda fargabar kama shi.
Mista Pascal Chbuoke ya gargadi masu yin fasa-kwauri da su daina ko kuma su fuskanci fushin doka.
Ya ce a cikin makonni hudu da suka gabata hukumar hana fasa kwauri ta jihar Neja Kogi ta kama wasu manyan motoci guda tara wadanda kudinsu ya kai naira miliyan dari da saba’in.
Sun mika buhunan dari biyu da tamanin da uku na kayayyakin da aka kama ga hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA kwamandan jihar Neja Shehu Gwadabawa domin daukar matakin da ya dace.
A jawabinsa bayan ya karbi kayayyakin Kwamandan NDLEA Shehu Gwadabawa ya yabawa sabon shugaban yankin bisa hadin gwiwa da rundunarsa tare da bayar da tabbacin cewa hadin gwiwar za ta ci gaba da samun ci gaba mai ma’ana.
KARSHEN ALIYU LAWAL/Wababe
-
Ilimi6 days ago
Gwamna Namadi Ya Nada Sabon Shugaban Hukumar Tsangaya Ta Jihar Jigawa
-
Labarai6 days ago
Kashim Shettima Ya Kaddamar da Majalisar Shawara ta Kasa Kan Tsaro
-
Labarai6 days ago
Shugaba Tinubu Ya Yi Ta’aziyya Ga Mele Kyari Kan Rasuwar ‘Yarsa
-
Labarai6 days ago
An Gaza Cimma Matsaya Tsakanin IPMAN Da NNPCL
-
Labarai4 days ago
Ambaliyar Ruwa: Gwamnatin Jigawa Ta Raba Tallafi A Karamar Hukumar Gwaram
-
Labarai6 days ago
Gwamna Radda Ya Ba Da Gudunmawar Dala Dubu 10 Ga Jamhuriyar Nijar
-
Labarai4 days ago
Jam’iyyar PDP Ta Kauracewa Zaben Kananan Hukumomi A Jihar Nasarawa
-
Labarai4 days ago
Gobara: ‘Yan Majalisar Zamfara Sun Jajantawa Shugaban Majalisar