Connect with us

Kasuwanci

Kwamitin Warware Turka-Turkar Dangote Da NNPCL Ya Fara Aiki

Published

on

Majalisar wakilai ta kaddamar da wani kwamitin hadin gwiwa na bangaren man fetur na gudanar da bincike kan kalubalen da ake fuskanta a fannin da kuma zargin samarwa da shigo da kayayyaki marasa inganci da gurbatattun danyen man fetur a cikin gida.

 

Mataimakin kakakin majalisar, Benjamin Kalu wanda ya bayyana haka, ya bukaci mambobin kwamitin da su gudanar da aikinsu cikin tsanaki ba tare da tsoro ko nuna son rai ba.

 

Ya jaddada cewa manufar ita ce samar da mafita mai ɗorewa kan zargin shigo da man da ba shi da inganci.

 

Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan taron mamba mai wakiltar karamar hukumar Birnin Kano kuma mamba a kwamitin hadin gwiwa Sagir Ibrahim Koki ya bayyana cewa bayan kaddamar da kwamitin kwamitin ya tattauna sosai kan batutuwa da dama tare da amincewa da rubuta wasikun gayyata ga dukkan masu ruwa da tsaki. da Hukumomin Gwamnati da abin ya shafa

 

Sagir Ibrahim ya ci gaba da bayyana cewa a yanzu kwamitin zai duba batutuwa talatin amma mafi muhimmanci daga cikinsu akwai zargin da ake yi tsakanin matatar man Dangote da hukumar kula da albarkatun man fetur, da batun shigo da gurbatattun danyen man fetur da kuma batun rashin wadata matatun mai na na cikin gida da danye mai.

 

Dan majalisar ya ci gaba da cewa, kwamitin ya kuduri aniyar gayyatar duk masu ruwa da tsaki a harkar man fetur musamman wadanda abin ya shafa don gudun kada a ce ba a ba wa wani damar kare kansa ba, yana mai tabbatar da cewa duk wadanda abin ya shafa dole ne su gurfana a gaban kwamitin don magance matsalar.

 

Bashir M/Wababe

Labarai

Labarai1 day ago

Ziyarar Shugaba Tinubu Zuwa China Ta Yi Nasara

  Ziyarar Shugaba Tinubu zuwa China Ta Yi Nasara, da kuma Shaida Wa ‘Yan Najeriya Mazauna China, Yi Alkawarin don...

Labarai1 day ago

Sabon Tsarin Albashi: Majalisar Kano Ta Amince da Karin Kasafin Naira Biliyan 99

Majalisar Dokokin Kano ta amince da ƙarin kasafin kudi na N99bn da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike mata domin...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Musanta Jita-Jitar Bayar Da Kudi Ga ‘Yan Ta’adda

  Gwamnatin Jihar Zamfara tayi watsi da jita-jitar da ke yawo cewar tana shirin bayar da kudi ga wasu sanannun...

Labarai2 days ago

Shugaba Tinubu Ya Dauki Matakan Gaggawa Don Wadata Man Fetur da Farashinsa

  Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Ɗauki Matakai Masu Ƙarfi don Magance Samuwar Man Fetur da Farashi a Faɗin Najeriya A...

Labarai2 days ago

Tinubu Ya Nemi Hadin Gwiwar Afirka da China Don Bunkasa Tattalin Arziki

  Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a ci gaba da hadin kai tsakanin Afrika da Sin, yana mai...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya ta Amince da Tsare-tsare Don Yakar Rashin Abinci Mai Gina Jiki

  Daga: Bello Wakili Ministan Tsare-tsare na Lafiya da Walwala ta Jama’a na kasa, Muhammad Ali Pate, ya jaddada muhimmancin...

Labarai3 days ago

ACF Ta Ce Babban Kalubalen Arewa Yanzu Shi Ne Rashin Tsaro

Kungiyar Tuntubar Arewa, wato Arewa Consultative Forum (ACF) ta ce a halin yanzu, batun da ya fi damun al’ummar arewacin...

Labarai3 days ago

Hukumar NOA Ta Yabawa Majalisar Jihar Nasarawa Wajen Samarda Dokoki Masu Amfani ga Jama’a

Hukumar Wayar da Kan Jama’a da Fadakarwa ta Kasa (NOA) ta yaba wa Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa bisa ga kafa...

Kasuwanci3 days ago

Shugaba Tinubu Ya Gana da Firayim Ministan Sin, Ya Ce Afirka Na Da Damar Zuba Jari da Haɓaka

  Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ce Afrika na da manyan damammaki wajen zuba jari, ci gaba, da haɓaka tare...

Labarai3 days ago

Tinubu Ya Jajantawa Jihar Yobe Kan Rashe-Rashen Rayukan da Aka Yi a Tarmuwa

  Shugaba Bola Tinubu ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Yobe kan rashin rayukan da aka yi a Mafa a...

Mafi Shahara