Connect with us

Ilimi

Jihar Jigawa Za Ta Gudanar Da Ayyuka Na Musamman A Bangaren Kiwon Lafiya

Published

on

Majalisar zartarwa ta jihar Jigawa ta amince da fitar da kimanin Naira Miliyan dubu uku domin gudanar da ayyuka a bangaren kiwon lafiya.

Kwamishinan yada labarai, matasa da wasanni da raya al’adu Alhaji Sagir Musa Ahmad ya bayyana haka ga manema labarai bayan kammala taron majalisar zartarwa ta jihar wanda Gwamna Umar Namadi ya jagoranta a gidan gwamnati.

Alhaji Sagir Ahmed ya bayyana cewar ayyukan da za a gudanar sun hada da katange harabobin manyan asibitoci da samar da wuta lantarki mai amfani da hasken rana a cibiyoyin kula da lafiya matakin farko guda 30.

Ya kara da cewar majalisar ta amince da fitar da naira miliyan dubu 3 da rabi domin aiwatar da shirin ba da tallafin rage radadin cutar corona da tada komadar tattalin arziki karkashin shirin noman fadama na 4 da na 5.

Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana cewar fiye da mutane dubu 30 ne za su ci gajiyar shirin.

Kazalika, majalisar zartarwar ta amince da kafa kwamitoci guda 2 domin mallakar jami’a mai zaman kanta ta Khadija University da ke Majiya a karamar Hukumar Taura dake Jihar

Kwamitocin sun hada da na kwararru karkashin jagorancin kwamishinan ma’aikatar ilimi mai zurfi, Dakta Isah Yusuf Chamo da na harkokin mulki karkashin jagorancin kwamishinan ilimi matakin farko Dakta Lawan Yunusa Danzomo.

 

Usman Mohammed Zaria

Labarai

Labarai1 day ago

Ziyarar Shugaba Tinubu Zuwa China Ta Yi Nasara

  Ziyarar Shugaba Tinubu zuwa China Ta Yi Nasara, da kuma Shaida Wa ‘Yan Najeriya Mazauna China, Yi Alkawarin don...

Labarai2 days ago

Sabon Tsarin Albashi: Majalisar Kano Ta Amince da Karin Kasafin Naira Biliyan 99

Majalisar Dokokin Kano ta amince da ƙarin kasafin kudi na N99bn da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike mata domin...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Musanta Jita-Jitar Bayar Da Kudi Ga ‘Yan Ta’adda

  Gwamnatin Jihar Zamfara tayi watsi da jita-jitar da ke yawo cewar tana shirin bayar da kudi ga wasu sanannun...

Labarai2 days ago

Shugaba Tinubu Ya Dauki Matakan Gaggawa Don Wadata Man Fetur da Farashinsa

  Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Ɗauki Matakai Masu Ƙarfi don Magance Samuwar Man Fetur da Farashi a Faɗin Najeriya A...

Labarai2 days ago

Tinubu Ya Nemi Hadin Gwiwar Afirka da China Don Bunkasa Tattalin Arziki

  Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a ci gaba da hadin kai tsakanin Afrika da Sin, yana mai...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya ta Amince da Tsare-tsare Don Yakar Rashin Abinci Mai Gina Jiki

  Daga: Bello Wakili Ministan Tsare-tsare na Lafiya da Walwala ta Jama’a na kasa, Muhammad Ali Pate, ya jaddada muhimmancin...

Labarai3 days ago

ACF Ta Ce Babban Kalubalen Arewa Yanzu Shi Ne Rashin Tsaro

Kungiyar Tuntubar Arewa, wato Arewa Consultative Forum (ACF) ta ce a halin yanzu, batun da ya fi damun al’ummar arewacin...

Labarai3 days ago

Hukumar NOA Ta Yabawa Majalisar Jihar Nasarawa Wajen Samarda Dokoki Masu Amfani ga Jama’a

Hukumar Wayar da Kan Jama’a da Fadakarwa ta Kasa (NOA) ta yaba wa Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa bisa ga kafa...

Kasuwanci4 days ago

Shugaba Tinubu Ya Gana da Firayim Ministan Sin, Ya Ce Afirka Na Da Damar Zuba Jari da Haɓaka

  Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ce Afrika na da manyan damammaki wajen zuba jari, ci gaba, da haɓaka tare...

Labarai4 days ago

Tinubu Ya Jajantawa Jihar Yobe Kan Rashe-Rashen Rayukan da Aka Yi a Tarmuwa

  Shugaba Bola Tinubu ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Yobe kan rashin rayukan da aka yi a Mafa a...

Mafi Shahara