Connect with us

Labarai

Jihar Jigawa Ta Kaddamar Da Kwamitin Sasanci Tsakanin Manoma Da Makiyaya

Published

on

Sakataren gwamnatin jihar Jigawa, Malam Bala Ibrahim ya kaddamar da kwamitocin zaman lafiya da sulhu domin tabbatar da zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya a Janwawa, da Bagadaza a kananan hukumomin Birnin Kudu da Gwaram.

Da yake jawabi a wajen kaddamar da kwamitocin, sakataren gwamnatin ya ce kafa kwamitocin na  nuni da aniyar  gwamnatin Umar Namadi na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’ummarta.

Bala Ibrahim ya lissafo wasu sharuddan da kwamitocin suka gindaya da suka hada da tabbatar da gaskiya da adalci wajen rabon filayen noma, labi da wuraren kiwo.

Ya kara da cewa aikin kwamitin ya hada da fadakar da manoma da makiyaya muhimmancin su ga al’umma da zaman lafiya.

Hakazalika, kwamitocin za su karfafa gwiwar bangarorin da ke rikici da juna don warware sabanin da ke tsakaninsu cikin ruwan sanyi.

Malam Bala Ibrahim ya ci gaba da bayyana ayyukan kwamitin, da suka hada da tabbatar da cewa manoma ba su kutsa kai ga duk wata hanya da za ta kai ga rafi ko kogi  don shayar da dabbobi.

Da yake mayar da martani a madadin kwamitocin biyu, shugaban kwamitin Janwawa na gundumar Sundumina wanda kuma shi ne jakadan Sulhu na Dutse, Alhaji Ado Ahmed ya nuna jin dadinsa bisa  nadin da aka masa tare da yin alkawarin bayar da gudunmawarsu duba da amincewarsa da aka kusi bisa hakan.

Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, mambobin kwamitocin sun hada da Alhaji Ado Ahmed,Fulani Shehu, Sale Babba, Musa Isah Bagadaza,Ya’u Haruna da Musa Maijama’a.

Sauran sun hada da Alhaji Abdu Salihawa, Maikudi Shanu, Adamu Janwawa, Amadu Jangari, wakilan ‘yan sanda, sojoji, jami’an tsaron farin kaya na DSS da NSCDC da dai sauransu.

 

Usman Muhammad Zaria

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Labarai1 day ago

Ziyarar Shugaba Tinubu Zuwa China Ta Yi Nasara

  Ziyarar Shugaba Tinubu zuwa China Ta Yi Nasara, da kuma Shaida Wa ‘Yan Najeriya Mazauna China, Yi Alkawarin don...

Labarai2 days ago

Sabon Tsarin Albashi: Majalisar Kano Ta Amince da Karin Kasafin Naira Biliyan 99

Majalisar Dokokin Kano ta amince da ƙarin kasafin kudi na N99bn da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike mata domin...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Musanta Jita-Jitar Bayar Da Kudi Ga ‘Yan Ta’adda

  Gwamnatin Jihar Zamfara tayi watsi da jita-jitar da ke yawo cewar tana shirin bayar da kudi ga wasu sanannun...

Labarai2 days ago

Shugaba Tinubu Ya Dauki Matakan Gaggawa Don Wadata Man Fetur da Farashinsa

  Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Ɗauki Matakai Masu Ƙarfi don Magance Samuwar Man Fetur da Farashi a Faɗin Najeriya A...

Labarai2 days ago

Tinubu Ya Nemi Hadin Gwiwar Afirka da China Don Bunkasa Tattalin Arziki

  Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a ci gaba da hadin kai tsakanin Afrika da Sin, yana mai...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya ta Amince da Tsare-tsare Don Yakar Rashin Abinci Mai Gina Jiki

  Daga: Bello Wakili Ministan Tsare-tsare na Lafiya da Walwala ta Jama’a na kasa, Muhammad Ali Pate, ya jaddada muhimmancin...

Labarai3 days ago

ACF Ta Ce Babban Kalubalen Arewa Yanzu Shi Ne Rashin Tsaro

Kungiyar Tuntubar Arewa, wato Arewa Consultative Forum (ACF) ta ce a halin yanzu, batun da ya fi damun al’ummar arewacin...

Labarai3 days ago

Hukumar NOA Ta Yabawa Majalisar Jihar Nasarawa Wajen Samarda Dokoki Masu Amfani ga Jama’a

Hukumar Wayar da Kan Jama’a da Fadakarwa ta Kasa (NOA) ta yaba wa Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa bisa ga kafa...

Kasuwanci4 days ago

Shugaba Tinubu Ya Gana da Firayim Ministan Sin, Ya Ce Afirka Na Da Damar Zuba Jari da Haɓaka

  Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ce Afrika na da manyan damammaki wajen zuba jari, ci gaba, da haɓaka tare...

Labarai4 days ago

Tinubu Ya Jajantawa Jihar Yobe Kan Rashe-Rashen Rayukan da Aka Yi a Tarmuwa

  Shugaba Bola Tinubu ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Yobe kan rashin rayukan da aka yi a Mafa a...

Mafi Shahara