Connect with us

Labarai

Dan Majalisa Ya Bukaci A Gaggauta Kafa Cibiyar Lafiya Ta Tarayya A Malam Madori

Published

on

Kudirin dokar kafa cibiyar kula da lafiya ta tarayya Malam Madori, wato Medical Centre a jihar Jigawa ya tsallake karatu na biyu a majalisar wakilai.

Dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Malam Madori/Kaugama Alhaji Abubakar Makki Yalleman ne ya dauki nauyin kudirin mai taken “Kudirin doka don gyara Dokar Cibiyoyin Kiwon Lafiya na Tarayya ta 2022.

Dan majalisar ya ce jihar Jigawa mai yawan al’umma sama da miliyan 5 ba ta da cibiyar kula da lafiya ta tarayya, wanda hakan ya tilastawa mazauna jihar yin tafiya mai nisa domin samun ingantaccen kiwon lafiya.

Ya tabbatar da cewa idan aka kafa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya ta Malam Madori, za ta magance matsalar kalubalen da ake fuskanta  a fannin kiwon lafiya a yankin, tare da samaun damar kulawar kwararru.

Alhaji Yalleman, ya bayyana cewa mazabar Malam Madori-Kaugama ta tarayya ta yi iyaka da mazabu kusan biyar a jihar Jigawa, an kuma samar da tituna da za su ka fa kowane yanki na jihar, amma sai al’ummar yankin sun je Nguru da je  jihar Yobe domin samun kiwon lafiya.

Bayan muhawara an amince da kudirin kuma an zartar da shi a karatu na biyu a zaman da mataimakin shugaban majalisar Mista Benjamin Kalu ya jagoranta.

 

Daga Salihu Tsibiri

Labarai

Labarai1 day ago

Ziyarar Shugaba Tinubu Zuwa China Ta Yi Nasara

  Ziyarar Shugaba Tinubu zuwa China Ta Yi Nasara, da kuma Shaida Wa ‘Yan Najeriya Mazauna China, Yi Alkawarin don...

Labarai2 days ago

Sabon Tsarin Albashi: Majalisar Kano Ta Amince da Karin Kasafin Naira Biliyan 99

Majalisar Dokokin Kano ta amince da ƙarin kasafin kudi na N99bn da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike mata domin...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Musanta Jita-Jitar Bayar Da Kudi Ga ‘Yan Ta’adda

  Gwamnatin Jihar Zamfara tayi watsi da jita-jitar da ke yawo cewar tana shirin bayar da kudi ga wasu sanannun...

Labarai2 days ago

Shugaba Tinubu Ya Dauki Matakan Gaggawa Don Wadata Man Fetur da Farashinsa

  Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Ɗauki Matakai Masu Ƙarfi don Magance Samuwar Man Fetur da Farashi a Faɗin Najeriya A...

Labarai2 days ago

Tinubu Ya Nemi Hadin Gwiwar Afirka da China Don Bunkasa Tattalin Arziki

  Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a ci gaba da hadin kai tsakanin Afrika da Sin, yana mai...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya ta Amince da Tsare-tsare Don Yakar Rashin Abinci Mai Gina Jiki

  Daga: Bello Wakili Ministan Tsare-tsare na Lafiya da Walwala ta Jama’a na kasa, Muhammad Ali Pate, ya jaddada muhimmancin...

Labarai3 days ago

ACF Ta Ce Babban Kalubalen Arewa Yanzu Shi Ne Rashin Tsaro

Kungiyar Tuntubar Arewa, wato Arewa Consultative Forum (ACF) ta ce a halin yanzu, batun da ya fi damun al’ummar arewacin...

Labarai3 days ago

Hukumar NOA Ta Yabawa Majalisar Jihar Nasarawa Wajen Samarda Dokoki Masu Amfani ga Jama’a

Hukumar Wayar da Kan Jama’a da Fadakarwa ta Kasa (NOA) ta yaba wa Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa bisa ga kafa...

Kasuwanci4 days ago

Shugaba Tinubu Ya Gana da Firayim Ministan Sin, Ya Ce Afirka Na Da Damar Zuba Jari da Haɓaka

  Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ce Afrika na da manyan damammaki wajen zuba jari, ci gaba, da haɓaka tare...

Labarai4 days ago

Tinubu Ya Jajantawa Jihar Yobe Kan Rashe-Rashen Rayukan da Aka Yi a Tarmuwa

  Shugaba Bola Tinubu ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Yobe kan rashin rayukan da aka yi a Mafa a...

Mafi Shahara