Connect with us

Labarai

Za’a Fara Wasannin Olympics A Faransa

Published

on

Yayin da ake dab da fara gasar wasannin motsa jiki ta bazara wato Olympic, ta shekarar 2024 a birnin Paris na ƙasar Faransa, al’amura na ci gaba da kan kama yadda ya kamata a matakai daban-daban, inda tuni aka gudanar da wasannin sada zumunci tsakanin  ƙasashe.

 

Duk da cewar wasan za’a ayyana buɗe shi a  jibi Juma’a 26, ga watan Yulin da muke ciki a hukumance, hakan ba zai hana karsashin magoya baya da ‘yan kallo ba , wajen cigaba da kallon wasanni masu ƙayatarwa biyo bayan fara wasannin.

A yau Laraba ne ake sa ran fara gudanar da wasan ƙwallon ƙafa da ƙwallon Zari Ruga ta ‘ƴan wasa 7 wato Rugby 7, Inda tuni ƴan wasa da ƙungiyoyin su, sun gama hallara tun a jiya.

A matsayin sharar fage za’a gudanar da wasan zari-ruga ta ƴan wasa 7, a yau ɗin, tsakanin tawagar ƙasashen da suka halarci gasar ta bana, kuma za a fara ne tun da misalin ƙarfe 3:30 na yammaci har zuwa ƙarfe 10 na daren yau, kuma duk wasannin za su gudana ne a filin wasa na Stede De France, kazalika a gobe Alhamis sauran tawagar za su fara fafata wa, tun daga misalin ƙarfe 2 na rana har zuwa ƙarfe 5 na yamma a zagayen farko, yayin da a zagaye na biyu kuma wasu jerin tawagar za su fafata tun daga misalin ƙarfe 8 na dare har zuwa ƙarfe 11 na dare.

A jibi Juma’a ne dai, za’a gudanar da bikin buɗe gasar inda ake sa ran mutane dubu ɗari 5 za su halarci kogin Sins da ya ratsa ta tsakiyar birnin Paris, kuma ƙasashe sama da 200 ne za su halarci wasannin.

Filayen da za a gudanar da ɗaukacin wasannin sun haɗa da Bercy arena, da porte de la chapelle arena da Paris La Defense arena, sai Aquatics centre da Stede de France da North Paris Arena da kuma Le Bourget sport climbing venue.

A wasannin na yau akwai ƙasashen Afrka guda 3 da zasu fafata a kwallon ƙafa 3 inda ake fatan za su bi sahnun Najeriya da Ghana wajen lashe lambobin zinari.

Bayanai sun ce an aike da jami’an tsaro sama da dubu ɗaya don bayar da tsaro a filin wasan da za’a kara tsakanin Mali da Isra’ila don tabbatar da tsaro yadda ya dace, kasancewar sa ɗaya daga cikin wasanni mafi ɗaukar hankali a yau.

Wannan shine karo na farko da Faransa ke ɗaukar nauyin gasar cikin shekaru 100 da suka gabata, lamarin da ke kara wa gasar armashi.

RFI

 

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Labarai

Labarai1 day ago

Ziyarar Shugaba Tinubu Zuwa China Ta Yi Nasara

  Ziyarar Shugaba Tinubu zuwa China Ta Yi Nasara, da kuma Shaida Wa ‘Yan Najeriya Mazauna China, Yi Alkawarin don...

Labarai1 day ago

Sabon Tsarin Albashi: Majalisar Kano Ta Amince da Karin Kasafin Naira Biliyan 99

Majalisar Dokokin Kano ta amince da ƙarin kasafin kudi na N99bn da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike mata domin...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Musanta Jita-Jitar Bayar Da Kudi Ga ‘Yan Ta’adda

  Gwamnatin Jihar Zamfara tayi watsi da jita-jitar da ke yawo cewar tana shirin bayar da kudi ga wasu sanannun...

Labarai2 days ago

Shugaba Tinubu Ya Dauki Matakan Gaggawa Don Wadata Man Fetur da Farashinsa

  Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Ɗauki Matakai Masu Ƙarfi don Magance Samuwar Man Fetur da Farashi a Faɗin Najeriya A...

Labarai2 days ago

Tinubu Ya Nemi Hadin Gwiwar Afirka da China Don Bunkasa Tattalin Arziki

  Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a ci gaba da hadin kai tsakanin Afrika da Sin, yana mai...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya ta Amince da Tsare-tsare Don Yakar Rashin Abinci Mai Gina Jiki

  Daga: Bello Wakili Ministan Tsare-tsare na Lafiya da Walwala ta Jama’a na kasa, Muhammad Ali Pate, ya jaddada muhimmancin...

Labarai3 days ago

ACF Ta Ce Babban Kalubalen Arewa Yanzu Shi Ne Rashin Tsaro

Kungiyar Tuntubar Arewa, wato Arewa Consultative Forum (ACF) ta ce a halin yanzu, batun da ya fi damun al’ummar arewacin...

Labarai3 days ago

Hukumar NOA Ta Yabawa Majalisar Jihar Nasarawa Wajen Samarda Dokoki Masu Amfani ga Jama’a

Hukumar Wayar da Kan Jama’a da Fadakarwa ta Kasa (NOA) ta yaba wa Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa bisa ga kafa...

Kasuwanci3 days ago

Shugaba Tinubu Ya Gana da Firayim Ministan Sin, Ya Ce Afirka Na Da Damar Zuba Jari da Haɓaka

  Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ce Afrika na da manyan damammaki wajen zuba jari, ci gaba, da haɓaka tare...

Labarai3 days ago

Tinubu Ya Jajantawa Jihar Yobe Kan Rashe-Rashen Rayukan da Aka Yi a Tarmuwa

  Shugaba Bola Tinubu ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Yobe kan rashin rayukan da aka yi a Mafa a...

Mafi Shahara