Connect with us

Ilimi

Shugaba Tinubu Ya Kaddamar Da Shirin Baiwa Dalibai Rance Na Naira Biliyan 33

Published

on

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yace ya cika daya daga cikin alkawarukan da yayi wa ‘yan Najeriya na kaddamar da shirin baiwa dalibai rance.

Shugaban kasan ya sanar da haka ne sa’ilin da yake kaddamar da shirin a Fadar Shugaban kasa dake Abuja.

Tun sa’ilin da yake yakin neman  zabe  shugaban kasan nan, Bola Ahmed Tinubu yayi alkawarin cewa zai yi kokari wajen ganin cl ‘yan kasa sun samu daman yin karatu musamman ‘ya’yan marasa karfi.

A dalilin haka ne wannan gwamnatin ta samar da shirin baiwa dalibai rance domin su samu damar yin karatu na zamani.

Da yake bayani yayin kaddamar da shirin shugaba Tinubu ya jaddada mahimmanci ilimi ga al’umma, inda ya ce  yana da matukar amfani wajen kawar da talauci a tsakanin al’umma, yana kuma sa hangen nesa da samar da cigaba da kuma inganta tsaro.

Shuagaban kasan yace gwamnati ta dukufa wajen zuba jari a harkar ilimi saboda yana taimakawa dan adam kyakkyawan buri da kuma samun damanmaki a rayuwa.

Ya kuma jaddada matsayin wannan gwamnatin na kyamar halin ko inkula a batun ilimi saboda sun san mahimmancinsa a rayuwar dan adam.

Yayi amannar cewa duk al’ummar da bata da wadataccen ilimi ko ta’addanci ba zata iya yaka ba bare samun wani cigaba mai ma’ana.

Shugaban hukumar bada rancen ga dalibai Akintunde Sawyer yace shirin zai cigaba da fadada ta yadda zai baiwa daliban kasar nan karin dama domin su yi karatu cikin sauki.

Ya kuma sanar da cewa yanzu haka sun bada naira biliyan talatin da uku ga dalibai dubu dari da goma a makarantun gaba da sakandari daban daban na fadin kasar nan.

A karshen taron shugaba Tinubu ya mika cakin  kudi ga wasu dalibai wadanda suka wakilci shiyoyi shida na fadin kasar nan, yayin da kuma ya sake mika wasu cakin  kudin ga wasu shugabannin makarantun gaba da sakandare a matsayin kudin makaranta na diliban da suka bukaci a biya musu kudin karatu wadanda suka haura dubu dari.

bello Wakili

Labarai

Labarai1 day ago

Ziyarar Shugaba Tinubu Zuwa China Ta Yi Nasara

  Ziyarar Shugaba Tinubu zuwa China Ta Yi Nasara, da kuma Shaida Wa ‘Yan Najeriya Mazauna China, Yi Alkawarin don...

Labarai2 days ago

Sabon Tsarin Albashi: Majalisar Kano Ta Amince da Karin Kasafin Naira Biliyan 99

Majalisar Dokokin Kano ta amince da ƙarin kasafin kudi na N99bn da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike mata domin...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Musanta Jita-Jitar Bayar Da Kudi Ga ‘Yan Ta’adda

  Gwamnatin Jihar Zamfara tayi watsi da jita-jitar da ke yawo cewar tana shirin bayar da kudi ga wasu sanannun...

Labarai2 days ago

Shugaba Tinubu Ya Dauki Matakan Gaggawa Don Wadata Man Fetur da Farashinsa

  Shugaban Ƙasa Tinubu Ya Ɗauki Matakai Masu Ƙarfi don Magance Samuwar Man Fetur da Farashi a Faɗin Najeriya A...

Labarai2 days ago

Tinubu Ya Nemi Hadin Gwiwar Afirka da China Don Bunkasa Tattalin Arziki

  Shugaba Bola Tinubu ya yi kira da a ci gaba da hadin kai tsakanin Afrika da Sin, yana mai...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya ta Amince da Tsare-tsare Don Yakar Rashin Abinci Mai Gina Jiki

  Daga: Bello Wakili Ministan Tsare-tsare na Lafiya da Walwala ta Jama’a na kasa, Muhammad Ali Pate, ya jaddada muhimmancin...

Labarai3 days ago

ACF Ta Ce Babban Kalubalen Arewa Yanzu Shi Ne Rashin Tsaro

Kungiyar Tuntubar Arewa, wato Arewa Consultative Forum (ACF) ta ce a halin yanzu, batun da ya fi damun al’ummar arewacin...

Labarai3 days ago

Hukumar NOA Ta Yabawa Majalisar Jihar Nasarawa Wajen Samarda Dokoki Masu Amfani ga Jama’a

Hukumar Wayar da Kan Jama’a da Fadakarwa ta Kasa (NOA) ta yaba wa Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa bisa ga kafa...

Kasuwanci4 days ago

Shugaba Tinubu Ya Gana da Firayim Ministan Sin, Ya Ce Afirka Na Da Damar Zuba Jari da Haɓaka

  Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ce Afrika na da manyan damammaki wajen zuba jari, ci gaba, da haɓaka tare...

Labarai4 days ago

Tinubu Ya Jajantawa Jihar Yobe Kan Rashe-Rashen Rayukan da Aka Yi a Tarmuwa

  Shugaba Bola Tinubu ya jajantawa gwamnati da al’ummar jihar Yobe kan rashin rayukan da aka yi a Mafa a...

Mafi Shahara