Connect with us

Labarai

Shugaba Tinubu Ya Rattaba Hannu Kan Kudirin Dokar Hukumar Raya Arewa Maso Yamma

Published

on

Shugaban kasa Bola Tinubu ya rattaba hannu  kan kudirin doka don hanzarta samar da ci gaba a shiyyoyin kasar nan.

Shugaban kasan ya amince da kudurin dokar hukumar raya yankin Arewa maso Yamma na shekarar 2024, da kuma kudurin hukumar raya Kudu maso Gabas na shekara 2023.

Za a kafa hukumar raya yankin Arewa maso yamma ne domin saukaka sake gina tituna, gidaje, da wuraren kasuwanci da rikice-rikice da dama suka lalata, tare da magance talauci, rashin neman ilimi, matsalolin da suka shafi muhalli, da duk wani abu da ke haifar da kalubalen  ci gaba a jihohin yankin Arewa maso yamma.

Bugu da kari, ita ma  hukumar raya shiyyar Kudu maso Gabas an kafa ta ne domin tabbatar da sake ginawa da gyara tituna, gidaje, da sauran barnar da shiyyar ta fuskanta, tare da magance matsalolin muhalli, da sauran matsalolin da ke kawo cikas ga ci gaba a jihohin Kudu maso Gabas.

Shugaba Tinubu ya yi amanna da gina al’umma bisa cikakken adalci, daidaito da kuma hadin kai; don haka ya himmatu wajen tabbatar da samar da ci gaba mai inganci, da gudanar da mulki tare da samar da ingantattun ayyuka ga daukacin ‘yan Najeriya

 

Daga Bello Wakili

Labarai

Ilimi18 hours ago

Gwamnati Za Ta Yiwa Madatsar Ruwan Alau Garanbawul A Barno

Gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na yin garambawul tare da tabbatar da madatsar ruwa ta Alau da ke Maiduguri a...

Fasaha18 hours ago

Majalisar Zartaswar Jihar Jigawa Ta Fitar Kudaden Tallafin Karatu

Majalisar zartaswa ta jihar Jigawa ta amince da kudi sama da naira miliyan dari bakwai da casa’in da takwas domin...

Labarai19 hours ago

Kungiyar Tsoffin Manyan Sakatarorin Zamfara Ta Sami Kyautar Mota

Gwamna Lawal Ya Ba Da Kyautar Mota Ga Ƙungiyar Tsaffin Manyan Sakatarorin Da Suka Yi Ritaya A Zamfara Gwamnan Jihar...

Labarai19 hours ago

An Tsinci Gawar Tauraron Mawakan One Direction Liam Payne

Liam Payne, ɗaya daga cikin mawaƙa a tawagar One Direction, ya mutu a Argentina bayan ya faɗo daga hawa na...

Labarai19 hours ago

Gwamnatin Tarayya Ta Jajantawa Wadanda Fashear Tankar Mai Ta Shafa A Jigawa

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bayyana matukar alhininsa dangane da mummunan fashewar tankar da ta afku a garin Majiya...

Ilimi19 hours ago

Hukumar Hisbah Ta Ziyarci Majalisar Dokokin Kano

Majalisar dokokin jihar Kano ta ce ta kuduri aniyar tabbatar da ingantattun tsare-tsare na walwala ga ma’aikatan Hisba domin tabbatar...

Fasaha20 hours ago

Za A Fafata A Gasar Tseren Doki Ta Masarautar Gwandu

Ana sa ran al’ummomin duniya daga Hadaddiyar Daular Larabawa da kasashen yammacin Afirka za su halarci gasar tseren doki na...

Kasuwanci20 hours ago

Gwamnan Niger Ya Kaddamar Da Shirin Kula da Lafiyar ‘Yan Fansho Da Tsofaffi

Gwamna Mohammed Umaru Bago na jihar Neja ya kaddamar da kunshin inshorar lafiya, wani shiri da aka tsara don samar...

Labarai20 hours ago

Kamala Harris Ta Yi Alkawarin Sauya Salon Mulkin Amurka Idan Ta Lashe Zabe

Ƴar takarar shugabancin Amurka a jam’iyyar Democrat, Kamala Harris, ta yi alƙawarin sauya salo daga irin kamun ludayin shugaba Joe...

Labarai4 days ago

Jam’iyyar PDP Ta Kauracewa Zaben Kananan Hukumomi A Jihar Nasarawa

Jam’iyyar PDP a Jihar Nasarawa ta ce ba za ta yi takara a zaben  kananan hukumomi da za a gudanar...

Mafi Shahara